Back

DA ƊUMI-ƊUMI: An Kashe Mutum Daya, An Rufe Kasuwa A Legas Sakamakon Hatsaniya

A safiyar ranar Juma’a ne aka dakatar da harkokin kasuwanci a kasuwar Oluwole da ke Ogba, a ƙaramar hukumar Ojodu a jihar Legas, yayin da aka yi artabu tsakanin Yarabawa da Hausawa.

An tattaro cewa rikicin ya ɓarke ne a daren ranar Alhamis ɗin da ta gabata inda wani matashi mai suna Abbey ya sasanta rikici tsakanin wasu Hausawa biyu, inda aka ce wani da ba a tantance ba ya daɓa masa wuƙa, inda ya bar shi cikin jina-jina.

Wasu shaidu sun bayyana cewa Abbey ya yi ta zubar da jini sosai kafin ya mutu, lamarin da ya haifar da ramuwar gayya tsakanin Yarabawa da Hausawa a yankin.

Harin na ramuwar gayya ya kai ga lalata kayan abinci da suka haɗa da barkono da albasa, da ‘yan kasuwan Hausawa ke sayarwa.

An ga motocin ‘yan sanda suna sintiri a kasuwar a ƙoƙarin da suke na daƙile rikicin da kuma dawo da zaman lafiya.

Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.

“Yi hakuri, ba zan iya amsa wannan kiran ba a yanzu,” ya rubuta a martani ga saƙon da aka aika masa kan lamarin.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?