Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya jagoranci dubunnan masu zanga-zanga zuwa majalisar dokokin ƙasar domin ƙorafe ƙorafensu kan tsadar rayuwa a ƙasar.
An ga jami’an tsaro daban-daban sun girke a sassa daban-daban na shiga da kuma fitan Majalisar Dokoki ta ƙasa musamman a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya domin gudanar da zanga-zangar.
Ana sa ran masu zanga-zangar da ke rera waƙoƙi za su isar da saƙon nasu ga shugabannin majalisar dokokin ƙasar.
Ƙungiyar ta NLC ta bijire wa gargaɗi da dama inda ta yanke shawarar ci gaba da zanga-zangar nuna rashin amincewa da matsalar tattalin arziƙin ƙasar.
A makon da ya gabata ne dai hukumar DSS ta yi gargaɗin cewa wasu mutane na shirin yin amfani da damar zanga-zangar da ƙungiyar ƙwadago ta shirya yi a ranakun ashirin da bakwai da ashirin da takwas ga watan Fabrairu domin tada rikici da tashe-tashen hankula.
Daraktan Hulɗa da Jama’a da kuma Dabarun Sadarwa na Hedikwatar DSS ta Ƙasa, Abuja, Dakta Peter Afunanya, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya yi kira ga ƙungiyar da ta yi watsi da matakin da ta ɗauka na zanga-zangar halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki domin samar da zaman lafiya.
Ya buƙaci da su ci gaba da tattaunawa da sulhu maimakon yin wasu abubuwa da ka iya tada zaune tsaye a ƙasar.