Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama mai suna “Take It Back Movement” ta yi zanga-zanga a titunan jihar Legas domin nuna rashin amincewa da tsadar kayan abinci da tsadar rayuwa a ƙasar.
An gudanar da wannan zanga-zangar ne duk da gargaɗin da kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Adegoke Fayoade, ya yi a ranar Lahadi.
An ga masu zanga-zangar ɗauke da alluna da rubuce-rubuce daban-daban a ƙarƙashin gada dake Ojuelegba a jihar domin bayyana kokensu kan halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki.