Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai kuma Shugaban Kwamitin Majalisar Akan Bitar Kundin Tsarin Mulkin Ƙasar, Benjamin Kalu, ya faɗa a ranar Litinin, ashirin da shida ga watan Fabrairu cewa sabon kundin tsarin mulkin Najeriya zai kasance a shirye nan da watanni ashirin da huɗu masu zuwa domin amincewar Shugaban Ƙasa.
Da yake jawabi a taron ƙaddamar da Kwamitin Majalisar kan bitar kundin tsarin mulkin ƙasar na shekara ta dubu daya da casa’in da tara, Kalu ya ce an yi shirin samar da sabon kundin tsarin mulki ne domin a bai wa shugaban ƙasa lokaci ya nazarci sauye-sauyen da aka samu kafin ya rattaba hannu a kai ya zama doka.
Ya ce: “Tsarin mulkinmu, ginshiƙin dimokuradiyyar mu, ya tsaya a matsayin shaida ga burinmu na samar da al’umma mai adalci da wadata. Amma duk da haka, yayin da muke fuskantar haƙiƙanin abin da ke faruwa a ƙarni na ashirin da ɗaya, ya zama wajibi a gare mu mu fahimci wajibcin yin sauye-sauye ga tsarin mulki, don tabbatar da cewa dokokinmu sun yi nuni da buƙatu da buri na jama’armu.”
Kalu ya ce kawo yanzu Majalisar ta karɓi ƙudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi; samun dama ga ma’adinai; ƙaruwar shigar mata cikin harkokin siyasa; bayyanan bayani na haraji ko tara da kowane matakin gwamnati zai karɓa da kuma samar da ofishin Magajin Garin Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ya ce wasu ƙudirorin doka da dama da aka zartar, amma shugaban ƙasa bai amince da su ba a yayin sauye-sauyen kundin tsarin mulki na biyar an dawo da su a gyaran da ake yi a halin yanzu, ciki har da ikon Majalisar Dokoki da Majalisun Jihohi na kiran Shugaban Ƙasa da Gwamnonin Jihohi, da kuma buƙatun gwamnati na jagorantar manufofi don tabbatar da haƙƙin samun abinci da wadatar abinci.
A cewarsa, hakan ya nuna sauyawan tsarin bitar kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma yadda yake da kyau wajen ƙarfafa dimokuradiyyar ƙasar, inda ya ƙara da cewa majalisar a shirye take ta karɓi ƙarin shawarwari don inganta tsarin mulkin ƙasa da kuma ƙarfafa dimokuradiyyar ƙasa.
Ya ce majalisar tana kuma jiran shawarwarin da za su gabatar da ƙudirin dokar da ke nuni da batutuwan da suka shafi ajandar sabon fatan Shugaban Ƙasa.
Ya amince da gyare-gyaren da aka yi wa kundin tsarin mulkin da majalisun da suka gabata suka yi, waɗanda suka haɗa da ‘yancin cin gashin kan Majalisun Jihohi da na Ɓangaren Shari’a na Jihohi; sake sunan “Gidan Kurkuku” a matsayin “Gidan Gyara Hali” sannan a canza su daga keɓantaccen jerin majalisu zuwa jerin majalisu na yanzu don ba da damar shiga ga jihar; canja wurin “hanyoyin jirgin ƙasa” daga keɓaɓɓen jerin majalisu zuwa jerin majalisu na yanzu; ba da damar jihohi su samar, su watsa, kuma su rarraba wutar lantarki a yankunan da cibiyar sadar da wutar lantarki ta ƙasa; sannan kuma ya buƙaci Shugaban Ƙasa da Gwamnoni su miƙa sunayen waɗanda aka zaɓa a matsayin Ministoci ko Kwamishinoni cikin kwanaki sittin da rantsarwa domin Majalisar Dattawa ko Majalisar Jiha su tantance su.
Ya ce kwamitin a shirye yake ya rungumi ƙalubale da damar da ke gabansa, ta hanyar amfani da ƙarfin fasahar ƙere-ƙere, kafofin sada zumunta, da haɗa kai, za mu tabbatar da cewa an ji kowace murya, an yi la’akari da kowane irin ra’ayi, kuma an baiwa kowane ɗan ƙasa damar shiga cikin tsara makomar ƙasarmu.
Ya ci gaba da cewa, “a yayin da zamu fara wannan tafiya, bari mu yi amfani da ƙwarin gwiwa daga kalaman manyan shugabannin da suka zo gabanmu. Mu tuna da hikimar Tafawa Balewa, wanda ya yi magana game da wajibcin haɗin kai da haɗin gwiwa a ƙoƙarinmu na gina kyakkyawar makoma.
“Bari mu sake jaddada aniyarmu ta tabbatar da dimokuraɗiyya, adalci da ci gaba. A tare, mu tashi tsaye wajen tunkarar kaluɓalen, mu gina kyakkyawar makoma ga Nijeriya, makoma mai kyau ta al’umma, daga al’umma, kuma don al’umma.