Back

DA DUMI-DUMI: Ƙungiyar Ɗalibai Ta Najeriya Ta Janye Shiga Zanga-Zanga, Ta Nemi A Tattauna

Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta bukaci kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da ta yi watsi da shirinta na Zanga-Zanga da ta shirya a yau da gobe tare da rungumar tattaunawa da gwamnatin tarayya.

A wata sanarwa da shugaban majalisar dattawan NANS, Akinteye Afeez ya fitar, ta ce yajin aikin za ta yi matukar illa ga dalibai, wadanda tuni ke fama da kalubale daban-daban a harkar ilimi.

Ya ce tabarbarewar kalandar karatu, jarabawa, da sauran ayyukan ilimi na iya kawo cikas ga ci gaban daliban da kuma kara ta’azzara halin da ake ciki a fannin ilimi

Kungiyar daliban ta jaddada muhimmancin hadin kai a lokutan rikici, inda ta bukaci kungiyar NLC ta hada kai da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki wajen ciyar da al’umma gaba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Gwamnatin Najeriya ta cika kusan kashi sittin cikin dari na bukatun da kungiyar NLC ta gabatar, wanda ke nuna aniyar magance matsalolin ma’aikata da kuma kyautata jin dadin su. 

Sai dai kuma barazanar yajin aikin da ke kunno kai na haifar da babbar barazana ta kara ta’azzara kalubalen tattalin arzikin da al’ummar kasar ke fuskanta da kuma kawo cikas ga rayuwar talakawan kasa ciki har da dalibai.

“Muna kira ga NLC da ta nisanta hanyar shiga yajin aikin tare da lalubo wasu hanyoyi na warware sabani da gwamnati. Mun yi imanin cewa tattaunawa da hadin kai mai ma’ana suna da mahimmanci don magance korafe-korafe da samun ci gaba mai ma’ana wajen kyautata jin dadin ma’aikata da ‘yan kasa baki daya.”

NANS ta yi alkawarin tallafa wa kungiyar ta NLC a kokarin da suke yi na magance kalubalen da ma’aikata ke fuskanta tare da tabbatar da walwala da wadata ga daukacin ‘yan Najeriya

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?