Back

Da Dumi-Dumi: Ƙungiyar kwadago Ta Najeriya Ta Sanar Da Zanga-Zanga A Duk Fadin Kasar

Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, Joe Ajaero ya bayyana wata zanga-zanga da za ayi ranaku biyu ana yi a duk fadin kasar. 

Shugaban kungiya ta NLC, ya bayyana haka ne a babban ofishin ƙungiyar da ke Abuja, a wani taron manema labarai a yau Juma’a.

Ƙungiyar ta ware ranakun ashirin da bakwai da ashirin da takwas ga watan biyu na wannan shekarar da su zame ranakun aiwatarwa.

Ƙungiyar ta bayar da dalilan yin hakan ne saboda, “cizon da ‘yan Najeriya ke sha na matsanancin ƙuncin rayuwa da ‘yan kasa ke fuskanta.”

Ya ce an yanke shawarar yin hakan ne domin halin rashi da wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki a halin yanzu.

A ranar tara ga watan nan ne ƙungiyar ƙodago Ta NLC da Kungiyar Kasuwanci, (TUC), suka bayar da wa’adin kwanaki goma sha hudu ga Gwamnatin Tarayya da su tabbatar da aiwatar da yarjejeniyoyi da gwamnatin da kungiyoyin suka kulla da ma’aikata domin saukaka wahalhalu da ƙuncin rayuwa a cikin kasar nan.

A biyo mu domin samun cikakkun bayanai nan gaba Kadan…..

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?