Back

Da Dumi-Dumi: Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano ta bankado maboyar kayan abinci

Hukumar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta rufe wasu maka-makan shaguna guda hudu da ke cike da dubban buhunan hatsi da sauran kayayyakin masarufi a jihar.

Maboyar kayan, wadanda ke kusa da unguwar Dawanau, kan hanyar Kano zuwa Daura har Katsina, an same su ne cike da masara, dawa, spaghetti, sukari, da taliya da ake kyautata zaton an boye kayayyakin masarufin ne domin su kara tsada a fito da su kasuwa a sayar .

Ba da jimawa ba, hukumar ta gargadi dillalan da ke tara kayan abinci a cikin birnin Kano da kewaye da su kaurace wa hakan domin zai iya kara tabarbarewar hauhawar farashin kayan abinci.

Da yake jagorantar tawagar jami’an tsaro da ‘yan jarida a ziyarar da suka kai ma’ajiyar, Shugaban Hukumar, Barista Muhuyi Magagi Rimin-Gado ya ce an boye kayayyakin ne domin kara hauhawar riba wanda hakan ke kawo yunwa a kasar nan.

A baya Rimin-Gado ya bayyana tara kayan abinci a matsayin haramun, tare da yin barazanar kamawa, tare da gurfanar da duk wadanda suka aikata wannan aika-aika da kuma duk wasu masu wata dabi’ar aikata laifuka masu kamannin haka wadanda za su iya haifar da karanci da hauhawar farashin kayayyaki.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?