Wata Kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta umurci, mai cece-ku-ce a TikTok,
Murja Ibrahim Kunya da ta je a duba lafiyar kwakwalwa ta a asibitin gwamnati.
Alkalin kotun, Nura Yusuf Ahmad ne ya bayar da umarnin a ranar Talata.
Nura Yusuf ya ce a lokacin bayyanar da ta yi a baya, an yi zargin cewa ba ta cikin koshin lafiya saboda zargin da ake yi mata na shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Kotun ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare ta a gidan yarin hukumar Hisba har sai an duba lafiyar ta.
Daga nan kotun ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar ishirin ga watan biyar na shekarar nan.