Back

DA DUMI-DUMI: ‘Yan Makarantun Ekiti, Malamai, Direba Da Aka Sace Sun Samu ‘Yanci

Wannan jarida ta samu labarin cewa daliban da aka sace a jihar Ekiti tare da direban su, da Malaman su wadanda lamarin ya shafa sun sake samun ‘yancin su da misalin karfe 2.00 na ranar Lahadi.

A cikin wani gajeren faifan bidiyo da wakilin mu ya samu, daliban da aka sako tare da malaman su suna zaunr a kasa, sun gaji kamar yadda wata uwa ta koka da halin da danta ke ciki a baya.

Jaridar ta ruwaito cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci Naira miliyan 100 domin a sako mutanen, amma ba a bayyana ko an biya kudin fansa ko a’a ba.

Wani jami’in gwamnati a Emure Ekiti, wanda ya tabbatar da sakin wadanda aka sace, ya ce “wadanda aka sace suna nan tare da  iyayensu da ‘yan uwan su. Zan ba ku cikakken bayani nan ba da jimawa ba.”

Wata majiya wacce kuma ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce jami’an ma’aikatar lafiya ta jihar suna nan, suna Kai kawo domin kai su Ado Ekiti babban birnin jihar domin kula da lafiyarsu.

A ranar Litinin da yamma ne wasu ‘yan bindiga suka sace wata motar bas tare da dalibai da wasu ma’aikatan makarantar zuwa maboyars su.

Kimanin mutane 10 ne da ke cikin motar bas din ‘yan makaranta biyar, malamai uku da direba  aka yi awon gaba da su.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai aka yi ta yada jita-jitar cewa an saki wadanda aka kame, lamarin da ‘yan sanda suka musanta.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?