Back

DA DUMI-DUMI: ‘Yan Sanda sun kama Mahdi Shehu kan ƙarar da tsohon ministan shari’a Malami ya shigar

‘Yan sandan Najeriya sun kama wani ɗan kasuwa haifaffen jihar Katsina kuma mai sukar gwamnatin Najeriya, Mahdi Shehu a Abuja.

Majiyoyi sun shaida wa SaharaReporters cewa an kama Mahdi Shehu ne a ranar Talatar da ta gabata bayan wata ƙara da ofishin shari’a na tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami (SAN) ya shigar a madadin tsohon ministan da iyalansa.

Wata majiya da ke kusa da Shehu ta tabbatar da kamawa da tsare shi ga a yammacin ranar Talata, inda ta ce ɗan kasuwan kuma mai fallasa bayanan, na hannun ‘yan sanda suna tsare da shi.

Majiyar tace, “An shaida min cewa an kama shi ne a bisa takardar koke da ofishin tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami ya rubuta a madadin Malami da iyalansa. Wasiƙar na rubuce ne bisa takarda da sa hannun shugaban ofishin lauyoyi na A.A. Malami & Co. Law Office kuma takardar ta kasance a madadin Malami da iyalansa.

“Sashen Sa Ido na Babban Sufeton ‘Yan Sanda (IGP) ne ya kama shi a Hedikwatar Rundunar da ke Abuja,” inji majiyar.

Majiyar, ta ƙara da cewa bashi da cikakken bayanin koken. Sai dai SaharaReporters ta gano cewa kamun nasa na da alaƙa da zargin da ya yi wa Malami a baya.

A halin da ake ciki dai, layukan wayar Shehu ba sa shiga a lokacin gabatar da wannan rahoton. Ba a iya samun shi ta hanyar waya.

A watan Yunin shekarar da ta gabata ne, Mahdi Shehu ya yi zargin cewa Malami da Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) na lokacin, AbdulRasheed Bawa sun yi ƙoƙarin amfani da tsarin sake fasalin Naira wajen kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, wanda zai tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu bai fito ba a matsayin Shugaban Ƙasa.

Ya yi kira da a kamo Malami bayan kama Bawa, inda ya wallafa a shafinsa na X cewa, “A KAMO MALAMI YANZU KO A SAKI BAWA SABODA: Shi ne ya zaɓe shi. Ya kula da shi. Ya yi masa jagora daga nesa. Malami ya shigar da ƙararraki ne da zaɓe. Ya sallami kuma ya wanke waɗanda ake zargin ta hanyar zaɓen wanda ya so. Ya yi watsi da umarnin kotu da dama. Ya raina ɓangaren shari’a.”

A cewar Shehu, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da wannan tsarin ba tare da sanin akwai wata ɓoyayyan manufa ba.

Ya kuma rubuta a shafinsa na X cewa, “Emefiele, Bawa da binciken da ake gudanarwa ya zuwa yanzu: Domin wasu lissafe-lissafen siyasa, Malami ya sa Bawa ya rubuta wasiƙa ga PMB yana ba da shawarar sake fasalin Naira.

“Malami ya amince da wannan saƙon kuma ya tura wa PMB, wanda ya umurci EME a makance da aiwatar da shi. Hakan ya kasance game da gwamnatin riƙon ƙwarya ne.” Cewar Shehu 

Tsakanin watan Sha daya zuwa watan Sha biyu na shekarar dubu biyu da ashirin, an kuma tsare Shehu na tsawon kwanaki 11 bisa umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda na lokacin, Mohammed Adamu.

Jami’an Sa Ido na Babban Sufeton ‘Yan Sanda (IGP) sun kama shi kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa Gwamnan Katsina na lokacin, Aminu Bello Masari, da Sakataren Gwamnatin Jihar a lokacin, Mustapha Inuwa, da sauran jami’ai da ‘yan kwangila.

Shehu, a cikin ƙarar da ya shigar gaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ya zargi gwamnati da almubazzaranci na Naira biliyan hamsin da biyu tsakanin shekara ta dubu biyu da Sha biyar zuwa shekara ta dubu biyu da ashirin da dai sauransu.

Amma Babbar Kotun Birnin Tarayya ta bayar da umarnin a saki Shehu a ranar 18 ga watan Sha biyu ba tare da bayyana kama mai ƙarar da tsare shi a matsayin haramtacce ba.

Daga nan ne kotun ta bayar da diyyar Naira biliyan 5 ga ‘yan sandan Najeriya da kuma sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya.

An sake kama Shehu kuma a ranar Sha shida ga watan biyu shekara ta dubu biyu da ashirin da daya, amma babbar kotun tarayya ta sake ba ‘yan sanda umarnin sakin Shehu daga inda suke tsare da shi.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?