‘Yan sanda dauke da makamai sun cafke shugaban jam’iyyar Labour Party (LP), Barista Julius Abure a yau ranar Laraba.
Abure na fuskantar zarge – zargen wawure kusan Naira biliyan uku na kudaden jam’iyyar.
Babu Cikakkun bayanai game da dalilan kama shi a garin Benin din cikin Jihar Edo har zuwa lokacin da aka rubuta wannan rahoton.
Sai dai hotuna sun bayyana a shafukan sada zumunta, inda suka nuna Abure yana zaune a kasa kafin ‘yan sandan su dauke shi a cikin .mota.
Cikakkun bayanai na tafe……