Back

DA DUMI-DUMI: ‘Yan ta’adda sun sako wata ‘yar NYSC, Direban mota a Zamfara bayan shafe watanni biyar a hannun su.

Hukumar NYSC a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin ta ce  hakan ya kawo adadin wadanda aka sallama zuwa biyar, yayin da ake ci gaba da kokarin tabbatar da cewa sauran ukun (mace daya da namiji biyu) har yanzu suna tsare. dawo da ‘yancinsu da wuri.”

Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) ta tabbatar da cewa rundunar soji ta samu nasarar sako wata ‘yar bautar kasa, ciki har da direban motar bas da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara a kan hanyar su ta zuwa sansanin NYSC da ke jihar Sakkwato a shekarar da ta gabata. 

Hukumar NYSCn a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin da ta gabata ta ce hakan ya kawo adadin wadanda aka sallama zuwa biyar, yayin da ake ci gaba da kokarin tabbatar da cewa sauran ukun da ke hannun ‘yan bindigan, mace daya da maza biyu samu dawowa.”

“Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa ta Kasa, Birgediya Janar YD Ahmed ya yaba wa jami’an tsaro bisa ga namijin kokarin da suka yi na samun nasarar, ya kara da cewa tsarin ba zai taba sauke nauyin da ya rataya a wuyan sa na tabbatar da jin dadin ‘yan yiwa kasa hidimar ba a kowane lokaci. , ”in ji Eddy Megwa, darektan yada labarai da hulda da jama’a.

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yi garkuwa da ‘yan yiwa kasa hidimar a hanyar su ta zuwa sansanin su a jihar Zamfara a watan Agustan na shekarar bara.

An tattaro cewa ‘yan kungiyar NYSCn na tafiya ne a cikin wata motar bas ta Akwa Ibom (AKTC) daga garin Uyo na jihar Akwa Ibom zuwa jihar Sokoto domin yi wa kasa hidima na tsawon shekara daya, sai ‘yan ta’addan suka tare motar ta su, suka yi awun gaba da su.

A watan goman da ya gabata, hukumar NYSC ta kuma sanar da cewa, sun ceto daya daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su.

Hakan na nufin har yanzu akwai akalla hudu daga cikin wadanda aka sace tare da ‘yan ta’addar.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?