Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ta ce rundunar sojin sama na Operation Hadarin Daji ta kai farmaki ta sama kan wasu ‘yan ta’adda biyu a wasu hare-hare a Katsina da Zamfara.
Harin na farko a ranar Talata ya shafi shugaban ‘yan ta’adda, Maudi Maudi, a kudancin Tsaskiya da ke ƙaramar hukumar Safana a jihar Katsina.
A cewar Daraktan Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai na NAF, AVM Edward Gabkwet, babu tabbas ko an kashe Maudi Maudi amma an kawar da wasu ‘yan ƙungiyar sa.
Gabkwet ya faɗa a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis cewa, tantance ɓarnar da aka yi bayan yaƙin ya nuna inda aka nufa ya ƙone da wuta, inda aka ga wasu tsiraru suna guduwa don tsira.
“Duk da cewa an kawar da ‘yan ta’adda da dama, har yanzu ba a tabbatar da cewa Maudi Maudi na cikin waɗanda aka kashe ba,” inji shi.
Gabkwet ya kuma ce an kai irin wannan harin a ranar Laraba a kan sarkin ‘yan ta’adda, Alhaji Na-Shama da ke ƙauyen Ussu a gundumar Nasarawar Mailayi a ƙaramar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara.
Ya ce ingantattun bayanan sirri na ɗan adam sun tabbatar da kashe wasu makusantan Na-Shama da kuma rusa sansani da dabarun sa gaba ɗaya.
A cewar sa, har yanzu ba a tabbatar da ko Na-Shama na cikin waɗanda abin ya shafa ba.
Ya ce, harin da aka kai ta sama yana taimakawa wajen kare rayukan fararen hula da kuma lalata sansanoni da dabarun ‘yan ta’adda.
“Wannan tsari ya yi daidai da manufofin Operation Hadarin Daji, wanda ya fi mayar da hankali kan kare yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya daga ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma fashi,” inji Gabkwet.