Back

Dakatar da Ningi ya ƙara rura wutar rikicin ƙarin kasafin kuɗi, inji Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci da a gaggauta gudanar da bincike kan zargin da ake yi na ƙarin kasafin kuɗi da ya rutsa da Majalisar Dattawa.

Atiku, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya gargaɗi Majalisar Dattawa da kada su haɗa baki da Gwamnatin Tarayya su hana jama’a shugabanci na gari musamman duba da halin da ƙasar nan ke ciki.

Hakan ya faru ne yayin da ya kuma yi Allah wadai da matakin da aka ɗauka kan Sanata Abdul Ningi, yana mai cewa dakatarwar ba tare da bincike ba ne kawai ke rura wutar rikicin.

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 ya ce: “A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, zarge-zarge sun tada zaune tsaye a Majalisar Dattawa, inda suka nuna shakku kan ingancin Dokar Kasafi ta 2024, ginshiƙin tsare-tsare da ci gaban ƙasarmu na shekara-shekara.

Ƙididdigar manufofin kasafin kuɗi da ƙungiyar bayar da shawarwari ta tabbatar da rashin gaskiya a cikin Dokar Kasafin 2024.

“Bugu da ƙari kuma, dakatarwar da aka yi wa Sanatan nan da nan ba da daɗewa ba, ba tare da cikakken bayani ba, ya ƙara rura wutar rikicin, ya bar mu da tambayoyi fiye da amsa.

“Ina buƙatar a yi cikakken bincike a kan waɗannan zarge-zargen. Kasafi ya ta’allaka ne a kan tsarin mulki, kuma duk wani kaucewa biyan buƙatun jama’a zai fuskanci adawa mai zafi. Ba za a amince da musantawa ba, kuma dakatarwar da aka yi wa wani Sanata ba zai iya rufe bakin zarge-zargen cin hanci da rashawa da kashe kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba da Gwamnatin Tarayya take yi.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce, “Ba tare da bayyana wa al’ummar Nijeriya cikakken bayani ba, dole ne mu ɗauki waɗannan zarge-zargen da ake yi musu: zamba. Gwamnati ba za ta iya yin watsi da zargin da ake yi na ƙarin kasafin kuɗin da ya kai naira tiriliyan uku da wasa ba.

Bisa la’akari da irin wahalhalun da al’ummarmu ke ciki a halin yanzu na yunwa, fatara, rashin tsaro, matsalar makamashi, rashin kwanciyar hankali, da tsadar rayuwa, jama’ar Nijeriya ba za su iya yin watsi da zarge-zargen da ke ƙara taɓarɓare yanayin tattalin arziƙin da muke da shi ba.”

Ya ce ‘yan majalisar tarayya a matsayinsu na zaɓaɓɓun wakilan jama’a, tsarin mulki ya ba su damar samar da doka don samar da zaman lafiya, oda, da shugabanci na gari, ba tare da haɗa baki da lalatattun mutane ba.

“Rashin yin hakan da dagewa da musantawa zai tabbatar da haɗin kan gwamnati a cikin munanan ayyuka a hukumance,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?