Back

Dala biliyan 10 ake buƙata duk shekara, don farfaɗo da fannin wutar lantarki, inji Ministan Wutar Lantarki

Ministan Wutar Lantarki, Mista Adebayo Adelabu

Ministan Wutar Lantarki, Mista Adebayo Adelabu, ya bayyana a Abuja jiya Litinin cewa Gwamnatin Tarayya na buƙatar dala biliyan 10 a duk shekara na tsawon shekaru 10 masu zuwa domin farfaɗo da fannin wutar lantarkin ƙasar.

Adelabu ya bayyana hakan ne a wajen zaman binciken da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Samar da Wutar Lantarki ya shirya kan buƙatar Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin kuɗin wutar lantarki da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC), ta yi.

Ya ce: “Don a farfaɗo da wannan fanni, gwamnati na buƙatar kashe aƙalla dala biliyan 10 a duk shekara a cikin shekaru 10 masu zuwa.

“Hakan ya faru ne saboda abubuwan da ake buƙata na samar da daidaito a fannin, amma gwamnati ba za ta iya biyan kuɗin ba don haka dole ne mu sanya wannan fanni ya zama abin sha’awa ga masu zuba jari da masu ba da lamuni.

“Don haka don mu jawo hankalin masu zuba jari, da zuba jari, dole ne mu sanya fannin ya zama abun sha’awa, kuma hanya ɗaya tilo da za a iya samar da hakan ita ce farashin kasuwanci.

“Idan har yanzu darajar tana kan naira 66 kuma gwamnati ba ta biyan tallafi, masu zuba jari ba za su zo ba.

“Amma yanzu da muka ƙara wa rukuni kuɗin wutar lantarki, akwai sha’awar masu zuba jari.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?