Back

Dalilin da ya sa ban yi musafaha da Gwamnan Kano ba, inji Ahmed Musa

Ahmad Musa da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

A sa’ilin da ake cece-kuce a kafafen sada zumunta kan wani faifan bidiyo da ke nuna yanayin gaisuwar sa ga Gwamnan Jihar Kano, kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa ya kare kansa.

Ya bayyana matakin da ya ɗauka a matsayin wata alama ta mutunta al’adu yayin da ya yi kira da a mayar da hankali ga matsalolin da ke addabar al’umma.

Kalaman Musa ya biyo bayan wani faifan bidiyo da ya shiga yanar gizo a ranar litinin inda ya nuna yadda yake gaisawa da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano yayin da ya ke yin biris da Gwamna Abba Yusuf, duk da cewa ya na rusuna masa.

Sai dai yayin da yake mayar da martani a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Musa ya ce, “Na lura cewa wani ɗan lokaci da aka ɗauka a faifan bidiyo kusan wata guda da ya wuce, ba zato ba tsammani ya zama abin cece-kuce a shafukan sada zumunta. Abin ban takaici ne ganin ana ruruta wani abu mai sauƙi na mutunta al’ada.”

Ɗan wasan wanda yake yin bayani akan ma’anar gaisuwar sa, ya jaddada tushen al’adun Arewa.

“A al’adunmu na Arewa, alamar durƙusawa, musafaha da sauransu na nuni da mafi girman mutuntawa. Wannan ita ce manufa ta lokacin da na gaida Mataimakin Gwamna a wannan yanayin.

“Amma a lokacin da na zo gaida Gwamna, na zaɓi na sunkuya, ban yi musafaha da shi ba, don girmama shi ta hanyar da ta ke da tushe a al’ada,” inji shi.

Musa ya ci gaba da nuna rashin jin daɗinsa kan yadda lamarin ya ɗauki hankulan jama’a har ma da kafafen yaɗa labaran ƙasar, inda ya karkatar da hankali daga wasu matsalolin da suka addabi ƙasar.

“Abin takaici ne cewa a cikin dukkan matsalolin da al’ummarmu ke fuskanta – matsalolin tattalin arziƙi, tsaro, faɗace-faɗacen addini, da sauran su – wannan ɗan ƙanƙanen lokacin da ba shi da muhimmanci ya ɗauki hankali sosai,” inji shi.

Tsohon ɗan wasan na Leicester City ya ƙara da cewa, “Abin da ya fi ban takaici shi ne kalamai kan mutuntawa ta, musamman daga waɗanda ba su san ni ba.”

Musa ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su karkatar da ƙarfinsu wajen nemo hanyoyin magance matsalolin da ke addabar ƙasar maimakon shiga cikin abubuwan da ba su dace ba.

“Mu dakata na ɗan lokaci mu yi tunani kan inda muka zaɓa don karkatar da ƙarfinmu. Shin bai kamata ya zama don neman mafita ga matsalolin da suka addabi al’ummarmu ba maimakon shiga cikin abubuwan da ba su dace ba?

“Ina roƙon mu duka da mu ba da himma don magance ainihin matsalolin da muke dasu. Mu mayar da hankali wajen ɗaukaka juna, samar da haɗin kai, da kuma yin aiki don makoma mai kyau ga kowa da kowa,” ya kammala.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?