
Aliko Dangote
Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afrika, Aliko Dangote, ya ce ya kamata ‘yan Nijeriya su yi tsammanin raguwar farashin kayayyaki idan aka yi la’akari da raguwar farashin man dizal.
Ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ya kai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu gaisuwar Sallah a gidansa da ke Legas.
“Na yi imani cewa muna kan hanya madaidaiciya. Na yi imani ’yan Nijeriya sun yi haƙuri kuma na yi imanin cewa abubuwa masu kyau da yawa za su samu a yanzu. Akwai ci gaba da yawa domin idan kuka duba, ɗaya daga cikin manyan matsalolin da muka samu shi ne faɗuwar darajar naira da ta yi tashin gwauron zabo har kusan naira 1,900.
“Amma a yanzu, mun dawo kusan naira 1,250, 1,300, wanda hakan ya yi kyau. Kayayyakin da yawa sun tashi. Idan ka je kasuwa, alal misali, wani abu da muke samarwa a gida kamar gari, mutane za su ƙara maka kuɗi. Me yasa? Domin suna biyan farashin dizal mai tsada sosai.
“Yanzu a matatar man fetur ɗin mu, mun fara siyar da man dizal a kusan naira 1,200 maimakon 1,650 kuma ina da tabbacin idan muka ci gaba da tafiya abubuwa za su ci gaba da inganta sosai,” inji Dangote.
“Wataƙila, nan gaba, duk da cewa farashin ɗanyen mai na hauhawa, na yi imanin cewa mutane ba za su samu hakan fiye da yadda yake a yau ba, naira 1,200. Zai iya zama ma ƙasa da hakan kaɗan, amma hakan na iya taimakawa sosai domin idan kuna jigilar kayan da ake samarwa a cikin gida kuma kuna biyan naira 1,650, yanzu kuna biyan kashi biyu bisa uku na adadin, naira 1,200. Yana da bambanci da yawa. Mutane ba su sani ba.
“Wannan na iya taimakawa wajen rage hauhawar farashin kayayyaki nan take. Kuma na tabbata lokacin da alƙaluman hauhawar farashin kayayyaki suka fito na wata mai zuwa, za ku ga cewa an sami ragi sosai a hauhawar farashin kayayyaki. Kuma na tabbata gwamnati tana aiki ba dare ba rana domin ganin al’amura sun yi kyau domin amfanin kowa da kowa ne al’amura su daidaita.”