Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote, ya ce matatar man Dangote ta rage farashin man dizal zuwa naira 1,000 a kowace lita domin a samu sauƙin samfurin da kuma rage tsadar kayayyaki ga talakawan ƙasar nan.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai jiya a Gombe bayan halartar ɗaurin auren ɗiyar abokin kasuwancinsa, Alhaji Umaru Kwairanga, Sarkin Fulanin Gombe.
Dangote ya ƙara da cewa yana da matuƙar muhimmanci a tabbatar da cewa farashin kayayyaki masu muhimmanci kamar dizal na da araha don rage wa mutane da ‘yan kasuwa matsalolin kuɗi da suke fuskanta wajen samar da kayayyaki da sufuri.
A cewarsa, farashin dizal mai araha zai taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar.
Ya bayyana cewa, ta hanyar rage farashin man dizal, ‘yan kasuwa za su samu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, wanda a ƙarshe zai haifar da ƙarin aiki, samar da ayyukan yi da rage farashin kayayyaki.
“Idan ka duba, dizal yana shafar rayuwar kowa da kowa. Farashin kayayyaki kamar tumatur a yau a Legas saboda tsadar sufuri ne; kuma wajen samar da wani abu, babban farashi shine dizal. Da muka duba, sai muka yanke shawarar ganin yadda za mu rage kuɗin,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa, akwai mutanen da suka daɗe suna yin sana’ar kuma suna cin riba, don haka suka yanke shawarar cewa man dizal bai kamata ya wuce naira 1,000 ba, wanda ya kai ragin kusan kashi 60 cikin ɗari.
“A wurare irin su Borno da Bauchi ana siyar da shi tsakanin naira 1,700 zuwa 1,800, amma ina da tabbacin nan da ‘yan kwanaki masu zuwa ba za ku sayi dizal a sama da naira 1,000 a ko’ina a Nijeriya ba,” inji Dangote.