Back

Dalilin da ya sa muke binciken basussukan El-Rufa’i, inji Kakakin Majalisar Dokokin Kaduna

El-Rufa’i

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Liman, ya bayyana dalilin da ya sa Majalisar ke binciken rancen da gwamnatin tsohon Gwamnan Jihar, Malam Nasir El-Rufai ta karɓa.

Liman ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata bayan da majalisar ta kafa wani kwamiti mai mutum 13 kan binciken gano gaskiyar hada-hadar kuɗi, rance da tallafi, da sauran ayyukan da aka aiwatar daga shekarar 2015 zuwa 2023 a gwamnatin El-Rufai.

Ya ba da tabbacin cewa za a duba lamarin yadda ya kamata, yana mai cewa za su baiwa kowa ‘yancin faɗin gaskiya.

“Muna so ne kawai mu yi nazari kan kuɗaɗen da gwamnatin da ta gabata ta kashe domin mu yi alfahari da samun ƙarfin gwiwa lokacin da muka gama majalisa, ba ma so wani ya kira mu ‘yan Majalisar da ke amincewa da duk wani abu ba tare da nazari ba, ba za mu yi wannan bincike don yin izgili ga kowa ba, amma za mu yi abin da ya dace,” inji shi.

Wannan na zuwa ne makonni biyu bayan da magajin Gwamna El-Rufai, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gaji bashin da ya kai dala miliyan 587, da naira biliyan 85, da kuma bashin kwangila 115 daga hannun gwamnatin El-Rufa’i.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?