Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar Labour (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi bayanin rashin halartar babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka kammala kwanan nan a Nnewi, jiharsa ta Anambra.
Da yake magana a wata tattaunawa da Parallel Facts suka shirya a ranar Asabar a kan X, Obi ya bayyana cewa ya fi sha’awar gina “sabuwar Nijeriya” fiye da gina sabuwar LP.
Ya nuna rashin jin daɗinsa da yadda Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) ƙarkashin jagorancin Julius Abure ya yi watsi da shawarar da ya bayar na ƙara neman shawara sakamakon matsalolin da masu ruwa da tsaki suka gabatar gabanin taron.
“Mun yi alƙawarin gina Nijeriya; ba mu yi alƙawarin gina Sabuwar Jam’iyyar Labour ba. Lokacin da shugaban majalisar ya tuntuɓe ni game da taron, sai na roƙe shi da ya tuntuɓi duk masu ruwa da tsaki, tun daga Gwamna Alex Otti, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa Yusuf Datti, da Sanatoci, ’yan Majalisar Wakilai, ’yan takarar gwamna, da sauran ƙungiyoyi domin mu samu NLC, TUC,” inji Obi.
“An rubuta mana cewa za mu yi babban taron da ya dace, tare da farawa da ƙananan tarurruka, saboda dole ne mu tsara kanmu a matakin farko, inda muke da matsaloli. Bayan mun shirya kanmu ne za mu iya yin babban taron,” inji shi.
Obi ya ƙara da cewa ya kamata a yi taron masu ruwa da tsaki inda za a amince da ra’ayoyi domin biyan buƙatu daban-daban da jam’iyyar ta ƙunsa, amma ba a yi hakan ba.