Back

Dalilin da yasa aka ɗage ƙaddamar da shirin lamunin ɗalibai, inji Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta yi ƙarin haske kan ɗage ƙaddamar da shirin bayar da lamuni na ɗalibai.

Babban Sakataren Asusun Tallafawa Manyan Makarantu, (TETFund), Sonny Echono, ne ya bayyana hakan a lokacin da Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya kai masa ziyara a Abuja, ranar Laraba.

Ya ce jinkirin ɗage shirin ba na sai baba ta gani bane, amma na tsawon makonni biyu ne.

Echono wanda ya tabbatar wa ɗaliban Nijeriya cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya jajirce kan aikin ya ce an samu tsaikon ne saboda wasu abubuwa da majalisar lura dasu.

Ya ce an samu tsaikon ne kawai domin a tabbatar da cewa ba a samu matsala wajen aiwatar da shirin yadda ya kamata ba da kuma tabbatar da cewa shirin ya yi daidai.

“Ba a ɗage wannan lamunin ba har abada, akwai kawai wasu gyare-gyare da ya kamata a yi ne, Shugaban Ƙasa na da shirye-shiryen ƙaddamar da shi,” inji shi.

Ya ce akwai yiwuwar ɗalibai 140,000 za su ci gajiyar shirin a shekara ta farko, kuma za su iya nema da zarar an ƙaddamar da shirin muddin sun samu gurbin karatu.

“Muna magana kan kwanaki ne, ko makonni don farawa. Shugaban Ƙasa ya jajirce matuƙa a kan hakan, kuma ina tabbatar maka da cewa za a yi hakan ta hanya mafi kyau. Ba ma so mu gaggauta ƙaddamar da shirin, kuma akwai masu adawa da shi, kuma ba mai ɗorewa bane”.

Muna kallon sama da ɗaliban da muke da su kuma muna shiga sashin fasaha. Muna tabbatar da cewa rancen zai iya ɗaukar yawancin waɗanda suke buƙata. Ko ga mutanen da ke da basira, zai zama mai canza wasa. Muna aiki kafaɗa da kafaɗa da JAMB, mun san lokacin da za a fara shiga, don haka ba mu yi nisa ba.

“A cikin makonni biyu masu zuwa, shirin zai fara aiki, kuma zai ɗauki kowa da kowa, har ma da ɗaliban koyon sana’a,” inji shi.

Tun da farko, Gwamna Abdulrazaq, ya yabawa Kwamitin Asusun Tallafawa Manyan Makarantu, TETFund, bisa kuɗaɗen shiga ga manyan makarantu a Kwara, ya kuma buƙaci a ƙara himma.

“Wani lokaci kuna yin abubuwan da ba mu gani ko bamu nema ba kamar misali a Kwara, muna da mafi kyawun ɗakin karatu na jami’a a Yammacin Afirka; gini ne mai ban mamaki, abin da zan iya cewa shine na gode,” inji shi.

“Ƙalubalen sun kasance musamman a fannin gudanarwa da ababen more rayuwa don saka hannun jari kuma muna da koma-baya inda ma’aikatan da ba su koyarwa a cikin waɗannan makarantu sun fi ma’aikatan ilimi yawa na waɗannan makarantu kuma suna cinye yawancin albarkatun da aka yi niyya ga makarantun kuma a nan ne kuka shigo kuma kuka zurfafa yerjejeniyar ku.”

Ya buƙaci Asusun da ya ƙara kaimi wajen magance ƙalubalen da ake fuskanta a kwalejojin ilimi a jihar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?