Back

Dandazon matasa sun yi bore a jihar Osun, domin halin kunci, tabarbarewar tattalin arziki, rashin tsaro a Najeriya.

Dandazon matasa sun fito kan titunan Osogbo, babban birnin jihar Osun, domin nuna adawa da tabarbarewar tattalin arziki da rashin tsaro a Najeriya.

Masu zanga-zangar dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce da dama, sun fito suna rera wakokin hadin kai don nuna korafe-korafen su, da kuma bukatar inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Mstasan sun hadu ne a unguwar tsohon garejin da ke cikin birnin inda suka tare manyan tituna kafin su wuce zuwa Freedom Park, Orisunmibare, Ola-Iya, Alekunwodo, sai kuma yankin Oke-Fia na babban birnin jihar.

A Lokacin boren, ‘yan sanda dauke da makamai sun kasance a a shirye domin tabbatar da bin ka’ida da doka da kuma hana zanga-zangar baiwa ’yan daba dama su yi aika-aika da dakile tashin hankali.

Jagoran masu zanga-zangar, Kwamared Waheed Lawal, ya koka da cewa manufofin gwamnati mai ci a yanzu, manufofi ne na adawa da mutane ba wai tana da alkiblar rage radadin da talakawa ke ciki bane.

Ya ce, “Dole ne gwamnati ta yi duk abin da ya kamata ta yi domin tabbatar da cewa jama’a sun ci gajiyar ta. Sun yi mana alkawarin gyara, amma abin da muke fuskanta a yanzu shi ne sabuntuwar wahalhalun.” inji shi.

“Abin da ‘yan Najeriya ke so shi ne yanayin zaman lafiya. Ba za mu so rashin tsaro ya ci gaba da addabar kasarmu ba, domin da halin rashin tsaro a kasar, ba za ka iya tafiya daga Osogbo zuwa Ibadan cikin kwanciyar hankalinka ba, za ka yi tunanin za a iya sace ka.”

“Mun fara wannan gwagwarmaya a yau kuma idan gwamnati ta yi kunnen uwar shegu, za mu ci gaba da jan hankalin jama’ar mu don su nuna kiyayyar su akan wadannan wahalhalun saboda abin ya ishe mu haka,” in ji shi.

Zanga-zangar tasu ta biyo bayan irin wanda aka yi a Minna, Jihar Neja, da Kano, duk a yankin Arewacin kasar nan.

Tun bayan hawansa karagar mulki a watan Mayu, Shugaba Tinubu ya kawo karshen bayar da tallafin man fetur da sarrafa kudade, lamarin da ya kai ga rubanya farashin man fetur da kuma tsadar rayuwa yayin da Naira ke zawarcin dala.

Ministocin kudi, yada labarai, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, da noma da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, daraktan babban bankin kasa da sauran manyan mataimakan Shugaban kasa ne suka halarci tarukan da aka fara ranar Talata domin neman mafita.

Ministan yada labaran Najeriya Mohammed Idris ya shaidawa manema labarai cewa, “Ya zuwa lokacin da aka kammala wadannan tarurrukan, za mu iya fitar da tabbatacciyar sanarwa kan mene ne matsayin gwamnati dangane da hakan.”

“Abin da zan iya cewa shi ne tattaunawa na ci gaba da gudana, kuma nan ba da jimawa ba za a iya samun mafita ga ‘yan Najeriya.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?