Back

Dangote, Adenuga, Rabi’u, Otedola sun shiga jerin sunayen masu biliyoyin kuɗi na Forbes

Daga hagu: Aliko Dangote, Mike Adenuga, AbdulSamad Rabi’u, Femi Otedola

Dangote, tare da wasu hamshaƙan attajirai uku na Nijeriya, sun samu matsayi a cikin jerin manyan attajiran duniya na shekarar 2024 na Forbes.

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya zo a matsayi na 129 da dukiyar da ta kai dalar Amurka biliyan 15.0, wanda ya tabbatar da matsayinsa na attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, kuma fitaccen ɗan kasuwa a duniya.

Forbes, kamfanin watsa labaru na duniya na Amurka, yana mai da hankali kan kasuwanci, saka hannun jari, fasaha, jagoranci, da salon rayuwa.

Tare da Dangote cikin jerin fitattun ’yan kasuwan Nijeriya akwai: Mike Adenuga, shugaban kamfanin Globacom, ya zo na 407 da arziƙin da ya kai dala biliyan 6.9; yayin da Abdulsamad Rabiu na Rukunin Kamfanonin BUA da Femi Otedola suka bi sahu; Rabi’u ya zo na 462 da dala biliyan 6.3, Otedola na 1906 da dala biliyan 1.7 a jerin.

Forbes ta tattara lissafin ta amfani da farashin hannun jari da farashin musaya tun daga Maris 8, 2024, inda ta tabbatar da sahihanci da dacewa.

Amurka ce ta mamaye jerin da manyan attajirai 813, inda take da haɗakar dala tiriliyan 5.7. China ta biyo bayanta da attajirai 473 da darajarsu ta kai dala tiriliyan 1.7, yayin da Indiya ta samu matsayi na uku da attajirai 200.

Adadin dukiyar attajirai na duniya ya kai dala tiriliyan 14.2 wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a shekarar 2024, wanda ya nuna ƙaruwar dala tiriliyan 2 daga bayanan shekarar da ta gabata.

Waɗannan alƙaluma sun nuna irin ɗimbin arziƙi da tasirin da manyan mutanen duniya ke da shi, suna nuna yadda tattalin arziƙin duniya ke ci gaba da bunƙasa da kasuwanci.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?