Back

Dangote ya sake rage farashin dizal da man jiragen sama zuwa naira 940 da naira 980

Aliko Dangote

Matatar man Dangote ta sake sanar da rage farashin man dizal da na jiragen sama zuwa naira 940 da naira 980 a kowace lita ɗaya.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake murnar rage farashin zuwa naira 1,000 makonni biyu da suka wuce.

Canjin farashin naira 940 ya shafi abokan cinikin da ke sayen lita miliyan biyar zuwa sama daga matatar, yayin da farashin naira 970 na masu sayen lita miliyan ɗaya zuwa sama ne.

Da yake magana game da sabon ci gaban, Shugaban Sashen Sadarwa, Mista Anthony Chiejina, ya bayyana cewa sabon farashin ya dace da ƙudurin kamfanin na rage illar matsalar tattalin arziƙi a Nijeriya.

“Zan iya tabbatar muku da cewa matatar mai ta Dangote ta haɗa gwiwa da gidajen mai da iskar gas na MRS, domin tabbatar da cewa masu amfani da man sun saye mai a farashi mai sauƙi, a dukkan gidajen man su na Legas ko Maiduguri. Za ku iya siyan dizal lita 1 akan naira 1,050 da kuma man jiragen sama akan naira 980 a duk manyan filayen jirgin da MRS ke aiki.”

Ya kuma bayyana cewa za a haɗa gwiwa da sauran manyan ‘yan kasuwar mai.

“Dalilin wannan shine a tabbatar da cewa masu saya ba sa saye a farashi mai tsada.

“Kamfanin Dangote ya himmatu wajen ganin ‘yan Nijeriya sun samu walwalavda jin daɗi don haka muna farin cikin sanar da wannan sabon farashin da fatan hakan zai taimaka matuƙa wajen rage tasirin matsalar tattalin arziƙi a ƙasar nan.

Idan dai ba a manta ba matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man dizal daga naira 1,200 zuwa naira 1,000 a kowace lita mako biyu kacal da suka wuce.

Wannan dai shi ne karo na uku da aka samu raguwar farashin dizal cikin ƙasa da makonni uku da aka sayar da kayan a kan naira 1,700 zuwa naira 1,200, sannan kuma aka rage farashin zuwa naira 1,000, yanzu kuma zuwa naira 940 da naira 980 kan farashin man jiragen sama a kowace lita.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?