Manyan jami’an tsaro a Kano sun ziyarci ƙaramar fadar da Alhaji Aminu Ado Bayero yake, inda tsohon Sarkin yake wata ganawa ta musamman dasu.
Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Sarki Muhammadu Sanusi kan kujerarsa wanda ya koma fadar da ke Ƙofar Kudu da safiyar ranar, amma da Ado Bayero ya koma jihar, ya koma ƙaramar fada bayan sa’o’i.
Gwamna Yusuf ya bayar da umarnin a kamo Ado Bayero amma ‘yan sanda sun ce za su bi umarnin da aka ba da na hana mayar da Sanusi.
Sai dai da alama Aminu Ado Bayero ya fi samun karɓuwa daga hukumomi domin rahotanni sun ce yana wata ganawa ta musamman da dukkanin manyan jami’an tsaron Kano amma har zuwa lokacin haɗaa wannan rahoto ba a san dalilan ganawar ba.