
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila da mai baiwa shugaban kasa, Bola Tinubu shawara akan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne suke jagorantar kwamitin shugaban kasa kan bada agajin gaggawa na abinci daga fadar shugaban kasa dake Abuja.
Ko da yake ba a bayyana jadawalin taron ba, amma labarin da aka tattaro yayi nuni da taron na da nasaba da zanga-zangar da ta barke a wasu sassan kasar Najeriya saboda tabarbarewar tattalin arziki.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da ministan kudi da kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin kasa, Wale Edun; Ministocin Ilimi, Dr Tahir Mamman, Ministan Aikin Noma da Abinci, Abubakar Kyari da ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris.
Haka kuma a taron akwai karamar ministar babban birnin tarayya Dr. Mariya Mahmoud; Karamin ministan noma da samar da abinci, Aliyu Sabi Abdullahi da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso.
Masu zanga-zangar a ranar Litinin sun toshe hanyar Minna zuwa Bidda, cike da cunkoson jama’a a babban dandalin Kpakungu tare da yin kira ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ta magance matsalar yunwa a kasar.
Kokarin da jami’an tsaro suka yi na dakile zanga-zangar ta hanyar harba barkonon tsohuwa tare da kama wasu masu zanga-zangar ya ci tura.
A wannan rana, matasan Kano suma sun yi zanga-zanga kan halin kunci, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da tabbacin zai kai kokensu ga shugaban kasa.