Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta bayyana sunayen sojojin da aka kashe a wani aikin sulhu, bayan wani rikici tsakanin al’ummar Okuama da Okoloba a Ughelli ta Kudu da ƙananan hukumomin Bomadi na jihar Delta.
An bayyana sunayensu ne a dandalin Whatsapp na Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro da ke Abuja.
Su ne kwamandan Bataliya ta 181 Laftanar Kanar Abdullahi Hassan Ali, Manjo SD Shafa, Manjo DE Obi, Kyaftin U Zakaria.
Sauran sun haɗa da Staff Sajan Yahaya Saidu, Kanal Yahaya Danbaba, Kabiru Bashir, L/Cpl Bulus Haruna, L/cpl Sole Opeyemi, L/Cpl Bello Anas, L/Cpl Hamman Peter da kuma L/Cpl Ibrahim Abdullahi.
Sun kuma haɗa da Pte Alhaji Ish, Pte Clement Francis, Pte Abubakar Ali, Pte Ibrahim Adamu, da Pte Adamu Ibrahim.
Blueprint ta ba da rahoto cewa aƙalla sojoji 16 da suka haɗa da Laftanar Kanal, Manjo biyu, Kyaftin ɗaya da sojoji 12 a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne wasu matasa suka kashe a gaɓar kogin Ijaw da Urhobo na jihar Delta.