Back

Direba ya gudu yayin da kwantena ta murƙushe wata mata har lahira a Legas

Wata babbar mota mai tsayin ƙafa 40 cike da kaya ta faɗo kan wata mota ƙirar Nissan mai lamba ABJ 692 BG, inda ta kashe wata mata nan take a yankin NNPC da ke Alapere a Jihar Legas.

Direban babbar motar da yaron motar sa sun tsere saboda tsoron kada wasu fusatattun mutane su kashe su.

Marigayiyar wacce ke zaune a bayan motar ta mutu nan take yayin da direban motar ya tsira da ransa.

Tuni dai aka ajiye gawar marigayiyar a ɗakin ajiyar gawa.

Daraktan Hulɗa da Jama’a da Wayar da Kai na Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA), Adebayo Taofiq, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Taofiq ya ce direban babbar motar da yaronsa sun gudu nan take da hatsarin ya afku.

Ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa direban babbar motar da ke cike da kaya yana cikin tsananin gudu ne a lokacin da ya rasa kan motar ya yi ciki-ciki da mota ƙirar Nissan da ke tafiya ta N.N.P.C da ke cikin Alapere, Ogudu a kan titin Legas zuwa Ibadan a Jihar Legas.

“LASTMA ta miƙa gawar ga ‘yan sanda daga ofishin ‘yan sanda na Alapere. Sauran masu bayar da agajin gaggawa a wurin da hatsarin ya afku sun haɗa da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASAMBUS), Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas da kuma ‘yan sanda.

“Haka nan a wurin da hatsarin ya afku akwai Babban Manajan LASTMA, Mista Olalekan Bakare-Oki; Daraktan LASTMA mai kula da al’amuran zirga-zirgar ababen hawa, sa ido kan abubuwan da suka faru, da tabbatar da bin doka, Mista Hakeem Adeosun da kuma tawagar ceto ta LASTMA,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?