Back

Dole ne mu ɗauki masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda, inji Tinubu

Tinubu tare da Alƙalin Alƙalan Nijeriya

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da ayyukan da masu garkuwa da mutane ke aikatawa a faɗin ƙasar, yana mai cewa dole ne a ɗauki waɗanda ke da hannu a irin waɗannan munanan laifuka a matsayin ‘yan ta’adda.

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Talata a liyafar cin abinci na watan Ramadan tare da mambobin ma’aikatan shari’a na tarayya ƙarƙashin jagorancin Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Olukayode Ariwoola.

Tinubu, wanda ya sake sabunta ƙudirin gwamnati na fatattakar ‘yan bindiga, ya ce waɗanda suka koma sace yara matsorata ne, waɗanda ba za su iya tinkarar ƙarfin sojojin Nijeriya ba.

“Dole ne mu ɗauki masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda. Su matsorata ne. An wulaƙanta su. Suna neman wurararen kai hari masu sassauci. Suna zuwa makarantu suna sace yara suna haifar da tashin hankali. Dole ne mu ɗauke su daidai a matsayin ‘yan ta’adda domin mu kawar da su, kuma na yi muku alƙawari za mu kawar da su,” inji Shugaban Ƙasar a wajen liyafar cin abincin da ya samu halartar jami’an shari’a masu yi wa ƙasa hidima da masu ritaya, ciki har da tsoffin Manyan Alƙalan Nijeriya guda biyu, Mai shari’a Mahmud Mohammed da Mai shari’a Walter Onnoghen.

Dangane da batun albashin ma’aikatan shari’a, shugaban ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren da suka dace don inganta walwala da yanayin aiki na jami’an shari’a.

Alƙalin Alƙalan Nijeriya ya yabawa gwamnatin ƙasar kan nasarar da ta samu ta hanyar naɗa alƙalai 21 a Kotun Ƙoli, lamarin da ya bayyana a matsayin wanda ba a taɓa yin irinsa ba.

Lateef Fagbemi, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, ya nuna godiya ga Shugaban Ƙasa kan miƙa ƙudirin dokar zartarwa mai taken “Ma’aikatan Shari’a, Albashi da Alawus da sauransu, Ƙudurin 2024” ga Majalisar Dattawa.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?