Back

Dole ne mu magance matsalar tsaro a kan iyakoki domin samun tsaron ƙasar – Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jaddada buƙatar magance matsalar rashin tsaro a kan iyakokin ƙasar domin samun damar magance matsalar tsaro da al’ummar ƙasar ke fuskanta.

Mataimakin Shugaban Ƙasar, wanda ya bayyana haka a wata ganawa da tawagar Hukumar Ci Gaban Al’ummomin kan Iyakokin Ƙasa (BCDA), ƙarƙashin jagorancin Babban Sakatarenta, Captain Junaid Abdullahi, a fadar shugaban ƙasa dake Abuja, ya kuma faɗi rawar da hukumar za ta taka wajen sauya yanayin tsaro a ƙasar.

Mataimakin Shugaban Ƙasar, ya yi alƙawarin ɗaukar matakin gwamnatin tarayya na tabbatar da tsaro da ci gaban al’ummomin kan iyakokin Najeriya don inganta rayuwar mazauna da kuma yanayin tsaro a ƙasar.

A cewar wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa, Stanley Nkwocha ya fitar, Shettima ya lura da ƙalubalen da waɗannan al’ummomi ke fuskanta da suka haɗa da rashin tsaro da rashin ababen more rayuwa.

“Yawancin ƙalubalen da muke fuskanta sun samo asali ne daga rashin tsaro a kan iyakokinmu, wanda ke bayyana a cikin shigowar makamai da harsasai ta iyakokin. Muna buƙatar mu yi magana akan rawar da BCDA za ta taka wajen sauya yanayin tsaro a kasarmu,” in ji VP Shettima.

Ya jaddada muhimmancin al’ummomin kan iyaka a cikin tsaron ƙasa tare da yin alƙawarin ci gaba da tallafawa buƙatun ci gaban su.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya amince da buƙatar mazauna yankin su ji cewa su ma ‘yan Najeriya ne tare da tabbatar da ƙudurin gwamnati na inganta harkokin kiwon lafiya da sauran muhimman ayyuka ga mazauna yankunan.

Shettima ya kuma buƙaci hukumar ta BCDA da ta samar da tsarin ƙarfafa hukumar, inda ya bayyana buƙatar ƙara tallafin gwamnati.

Babban Sakataren Hukumar, Captain Abdullahi, ya amince da ƙalubalen ƙarancin kayan aiki, ya kuma bayyana fatan cewa a ƙarƙashin jagorancin Shettima, hukumar za ta samu tallafin da ya dace domin cika aikinta.

Ya ce, “Al’ummomin kan iyakokinmu suna jin an ware su da sauran sassan ƙasar saboda rashin kula da su. Idan za mu iya samun ci gaba a cikin al’ummomin kan iyakokinmu, matsin lamba a cibiyar zai ragu. Da mun rage ƙaura daga ƙauyuka zuwa birni da kuma magance yawancin matsalolin mu na tsaro.

“A ƙarƙashin shugabancinka, mun yi imanin cewa bisa ayyukan ka a matsayinka na Gwamnan Jihar Borno, muna da tabbacin za ka ba mu tallafin da ake buƙata don ganin an ba wa hukumarmu kuɗaɗe domin gudanar da aikinta.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?