A watan da ya gabata, Kwamitin da ke Kula da Asusun Ajiya na Tarayya (FAAC), ya sanar da rabon naira tiriliyan 1.15 na kuɗaɗen shiga ga matakai uku na gwamnati a watan Fabrairun 2024, wanda ya nuna ƙarin naira biliyan 20 (kashi 1.77) daga naira tiriliyan 1.13 da aka ware a watan Janairun 2024.
Ƙarin ya nuna kyakkyawan sauyi a hanyoyin samun kuɗin shiga na ƙasar, kamar yadda Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Bawa Mokwa, ya yi bayani a ofishin Akanta Janar na Tarayya.
Hukumar ta FAAC ce ke da alhakin nazari da kuma raba kuɗaɗe ga jihohin gwamnatin tarayyar Nijeriya.
Dubi cikakken jerin rabon ga kowace jiha na Fabrairu 2024 a ƙasa: