Back

Duk da gargaɗin hukumar JAMB, an kama wani mahaifi yana rubuta wa ɗansa jarabawa

An kama wani uba tare da ɗansa saboda uban yana rubutawa ɗan nasa Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare (UTME) ta JAMB duk da gargaɗin da aka yi tun farko, inji Magatakardar Hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede.

Farfesa Oloyede da ya ke jawabi yayin ziyarar duba cibiyoyin UTME da ke Kaduna a cibiyar jarabawar ta Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) a ranar Laraba, ya ce an gudanar da jarabawar 2024 da kyau, sai dai an samu wasu ‘yan matsaloli na basaja, wanda hakan ya yiwu ne saboda a yanzu wasu suna da Lambar Shaida ta Ƙasa (NIN) fiye da guda ɗaya.

Ya kuma yi gargaɗin cewa za a kama waɗanda suka yi maguɗin jarrabawa a yanzu ko kuma bayan kammala jarrabawar, inda ya ce hukumar ta JAMB ta inganta fasahar ta domin duba waɗanda ke da hannu a duk wata maguɗi ta jarabawar.

Ya ce, “Ga waɗanda ke maguɗi, su sani ba ta biya. Fasahar tana taimakawa don bincika hakan a duk faɗin ƙasar, yawancin matsalolin da muke da su shine basaja. Misali yanzu, mun ce muna da NIN, yanzu muna da mutanen da ke da NIN guda biyu kuma hakan ya karya manufar tantancewa. Za mu warware hakan tare da NIMC.

“Muna da shari’ar wani uba ya yi basaja a matsayin ɗansa, yana rubuta wa yaron jarrabawa kuma na yi mamaki, ‘ba ka lalata makomar ɗanka ba?’ Yanzu haka an tsare su biyun. Ba zan iya fahimtar abin da uban zai gaya wa ɗansa ba lokacin da suke kulle a cikin ɗakin ajiye firsinoni ɗaya.

“Ba a Kaduna abun ya faru ba, amma ba na son bayyana jihar. Yawanci basaja ne, amma muna gabansu; muna ɗibar su kamar kaji, domin kayan aiki suna nan domin mu ga abin da suke yi, mu kuma kama su,” inji shi.

Magatakardar JAMB ɗin ya sanar da waɗanda suka faɗi jarrabawar saboda dalilan da ba na JAMB ba da su manta da jarrabawar, inda ya ce hukumar ta JAMB ba za ta iya kashe dubun-dubatar dukiyar al’ummar ƙasar nan ba wajen sake shirya wani zama na ‘yan takarar da suka kasa cin jarrabawar saboda rashin riƙon sakainar kashi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?