
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani dan bindiga mai suna Isah Lawal dan shekara 33 tare da shanu hamsin da biyar da tumaki shida a lokacin da yake shirin kafa wani sansanin ‘yan fashi a Kano. Mataimakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abdullahi Haruna ne ya bayyana haka a ranar Litinin.
Wanda ake zargin a cewar rundunar ‘yan sandan wani mazaunin kauyen Kaya ne da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.
Rundunar ‘yan sandan, tace wanda Ake zargin ya amsa cewa sun tsere ne daga sansanin ‘yan fashin su da ke yankin Maidaro cikin karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna saboda kashe daya daga cikin shugabannin kungiyar da bar su Mai suna, Bashir na garin Malumfashi a jihar Katsina wanda aka kashe a yayin arangama da wata kungiyar ‘yan bindiga da ke kishiryar su wanda hakan ya tilasta masa yanke shawarar komawa jihar Kano domin ya kafa sansani a yankin Gwarzo zuwa Karaye.
‘Yan sandan sun ce ana ci gaba da gudanar da sahihin bincike yayin da wanda ake zargin ke bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka wa ‘yan sanda wajen magance shigowarr ‘yan bindiga da masu aikata sauran laifuka shigowa jihar Kano da sauran jihohin da ke makwabtaka.
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel ya bayar da umarnin tura karin ma’aikata da kayan aiki zuwa dukkan iyakokin jihar Kano.
Kwamishinan ya bukaci kowa da kowa da ya ci gaba da kai rahotonin duk wani motsi na mutum ko wani abu da ya samu zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.