Back

EFCC ba ta gayyace ni ba, in ji tsohon shugaban hukumar alhazai ta kasa, ya yi barazanar daukar matakin shari’a

Tsohon Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) Zikrullah Hassan ya musanta rahotannin cewa jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) sun tuhume shi a ranar Litinin din da ta gabata kan zargin cin zarafi na ofis.

Hassan, wanda ya yi magana ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Shakirudeen Bankole, ya bayyana cewa babu wani lokaci da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gayyace shi domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen cin hanci da rashawa ko kuma wani laifi da ke da alaka da shi.

Yayin da yake tabbatar da cewa jami’an hukumar sun binciki litattafan hukumar a lokacin yana kan karagar mulki, yayin da jami’an hukumar ta NAHCON suka bayar da dukkan amsoshin tambayoyin da jami’an EFCC suka yi.

“Da girma na a matsayi na na musulmi kuma dan uwa na gari, da karfin gwiwa ta na ke so in tabbatar da cewa ba sau daya jami’an EFCC da ke aikin bincike a NAHCON suka ga ya zama dole su yi min tambayoyi ba game da ayyuka na ba Kuma same ni da wani laifi ba.”

“Ba za ku iya samun wata shaida ta mu’amala ta da ‘yan kwangila ba, ko na gudanar da wani ciniki na kuɗi face bisa tsarin ayyuka na dokokin hukumar.”

“Idan za su sake gudanar da binciken su sau goma ko fiye da haka, sakamakon zai kasance iri daya ne dai, domin ba na tsoma baki kan ayyukan da ba hurumin dokoki ba ne, musamman kasancewa ta kwararre,” in ji shi.

Da yake tabbatar wa al’ummar musulmi da sauran al’ummar cewa yayi aikin shi cikin gaskiya a lokacin da yake kan karagar mulki, Hassan ya yi alkawarin cewa nan ba da dadewa ba tawagar lauyoyin shi za su nema ma shi hakkin shi a kan mawallafin shafin yanar gizo da ke kokarin bata mishi suna da karya.

Dangane da liyafar karramawar da kungiyar Muslimi Companion ta shirya a kwanakin baya, Hassan ya kara da cewa, babban abin kunya ne a ce kafar yada labarai ta yi murnar rashin halartar wasu mutane da jami’ai.

A cewar shi, duk da cewa shi dan Muslim Companion ne, shi ma an gayyace shi zuwa liyafar ne kamar sauran baki duk da an zabe shi domin karramawa saboda kasancewar shi jakadan da ya cancanta

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?