Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce tana farautar, Margaret Emefiele, matar tsohon gwamnan babban bankin Najeriyan da wasu mutane uku ruwa a jallo.
Matar Emefiele, Eric Odoh, Anita Omoile da mijinta, Jonathan Omoile, an gurfanar da su a daren Juma’a bisa zargin hada baki da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN “don sauya makudan kudade mallakin gwamnatin tarayyar Najeriya tare da aikata laifin ta hanyar samun kudi bisa hanyar karya, da sata, sabanin hukunci da ke karkashin sashe na 411, 287, da 314 na dokar laifuka ta jihar Legas.”
Cikakkun bayanai na laifukan da ake zarginsu da aikatawa sun fito ne daga hukumar EFCC a wani hoton hoton mutanen hudu da aka kama a daren Juma’a.
Takardar ta ce, “Hukumar EFCC na neman mutum hudu Eric Odoh, Margaret Emefiele, Anita Omoile da Jonathan Omoile bisa laifukan da suka shafi tattalin arziki da kuma kudi. Akwai bayanai akan inda suke? Don Allah a tuntubi Hukumar EFCC mafi kusa ko ofishin ’yan sanda mafi kusa,.”
Wata takarda da EFCC ta fitar ta nuna cewa EFCC na tuhumar tsohon Gwamnan Baban bankin CBN, Emefiele ne bisa zargin almundahanar ₦ 1.8bn da $6.2m.
A halin da ake ciki, a karo na uku gwamnatin tarayya ta yi gyara a tuhume-tuhumen da ta ke yi wa Emefiele.
A tuhume-tuhume na baya-bayan nan da aka yi wa gyara a gaban mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotun birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, Hukumar EFCC ta zargi Emefiele da yin kamanceceniya da sakataren gwamnatin tarayya kan karbar $6.2m ba bisa ka’ida ba.
A bisa gyaran da aka yi wa tuhumar mai lamba CR/577/2023, Emefiele, a ranar 8 ga Fabrairu, 2023, ya hada baki da wani Odoh Ocheme, wanda a halin yanzu yake kan hanyarsa ta samun dala miliyan 6.2 daga bankin CBN, yana mai cewa sakataren Gwamnatin Tarayya ne ya bukaci hakan bisa wata wasika da ya gabatar mai kwanan wata 26 ga Janairu 2023 tare da Ref No. SGF.43/L.01/201.”
A cewar EFCC, Emefiele ya yi ikirarin cewa sakataren Gwamnatin Tarayyar ya bukaci babban bankin da ya saki “wasu kudi dala miliyan shida da dubi dari biyu da talatin ($6,230,000.00) bisa umurnin shugaban kasa na lokacin.”
EFCC ta ce Emefiele ya yi wannan ikirarin ne duk da sanin cewa karya ce, “kuma ka aikata laifin da ya saba wa sashe na 1 (1) na dokar zamba da sauran laifuffuka masu alaka da zamba, ta 2006, kuma za a hukunta ka a karkashin sashe na 1(3) na wannan Dokar.”
Har yanzu a cikin tuhumar da aka yi wa gyaran fuska, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta yi zargin cewa Emefiele, a watan Janairun 2023, ya kirkiri takarda mai suna: “Re: Presidential.directive on foreign election observers mission” mai kwanan wata 26 ga Janairu, 2023 tare da Ref No. SGF.43/L .01/201.
Ya ce an yi zargin hada baki da Ocheme da ke gudun hijira don aikata Hakan “ba bisa ka’ida ba”
Bugu da kari kuma, ana zargin Emefiele da baiwa matarsa, Omoile Margret, da kuma surukinsa, Omoile Macombo, cin hanci da rashawa, ta hanyar bayar da kwangilar gyaran wani yanki na gidan Gwamnan Baban bankin da ke Legas kan kudi militan casa’in da Tara da dubu dari takwas (N99.8m)
Hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta yi zargin cewa kwangilar gyaran masaukin Gwamnan Babban Bankin da ke Lamba 2 Glover Road, Ikoyi, Legas, an ba wani kamfani ne mai suna Messrs Architekon Nigeria Limited, “inda mutanen biyu suka zama daraktoci masu rinjaye da masu hannun jari.”
Hukumar EFCCn ta ce matakin da ake zargin Emefiele, ya saba wa sashe na 19 na dokar cin hanci da rashawa da sauran laifukan da suka shafi doka ta 2000.
Takardar tuhumar da aka yi wa kwaskwarima ta kunshi jimillar tuhume-tuhume 20 a kan Emefiele.
Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar Juma’a domin Emefiele ya daukaka kara kan tuhume-tuhumen da aka yi masa.
A farkon tuhumar da aka yi masa a watan Agustan 2023, an zargi Emefiele da laifin zamba har ta N6.5bn.
Sannan an gurfanar da shi tare da wata ma’aikaciyar CBN, Sa’adatu Yaro, da kamfaninta mai suna Afrilu 1616 Investment.
Daga baya EFCC ta yi gyara a tuhume-tuhumen ta hanyar rage laifuffukan zuwa shida, tare da cire sunayen Yaro da na Afirilu 1616 Investment, sannan ta rage adadin kudaden da ake zargi da zamba zuwa N1.2bn.
An gurfanar da Emefiele ne a kan tuhuma ta biyu a ranar 29 ga Nuwamba, 2023, kuma ya ki amsa laifin sa.
Daga nan ne EFCC ta bude shari’ar ta kuma kawo yanzu ta gabatar da shaidu uku gabannin gyara na baya-bayan nan.
Hukumar EFCC na farautar matar tsohon Gwamnan baban bankin Najeriya, Emefiele, wasu mutane uku