Back

EFCC ta kama fasto kan zargin zambar naira miliyan 3.9 a Ilorin

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta kama wani faston cocin Ilorin, Prophet Adeniyi James, bisa zargin damfarar wani ɗan cocin sa naira miliyan 3.9.

James shi ne Babban Mai Kula da Cocin Apostolic Christ (CAC), Freedom City Prophetic and Deliverance Ministry a Ilorin.

A wata sanarwa da ya fitar a Ilorin a ranar Asabar, shugaban yaɗa labarai na hukumar, Dele Oyewale, ya bayyana cewa hukumar EFCC shiyyar Ilorin ta kama James a ranar 2 ga Afrilu kan laifin.

Oyewale ya ruwaito wanda abin ya faru dashi, Oluwole Babarinsa, yana bayyanawa a cikin wata takardar koke ga hukumar, cewa James ya kira shi a lokacin wani shiri na coci a wani lokaci a 2021 kuma ya yi iƙirarin cewa yana da wahayi cewa (wanda abin ya faru dashi) zai fita ƙasar waje.

“Mai shigar da ƙarar ya bayyana cewa faston, a yayin da yake ba da wahayin, ya tambaye shi game da ƙasar da ya fi so, inda ya amsa da cewa, ‘Kanada’ kuma sun amince su tattauna daga baya domin a kammala shirin tafiyar.

“Mai shigar da ƙarar ya bayyana cewa daga baya James ya shaida masa cewa yana da wani abokinsa a Legas da zai taimaka masa wajen sauƙaƙa masa komawa ƙasar Canada, amma a kan kuɗi naira miliyan 1.7, da kuma naira miliyan 2.5 don sarrafa tikitin jirgi da takardun tafiya bi da bi.

“Babarinsa ya ƙara da cewa sai da ya sayar da wasu kadarorinsa, ya kuma karɓi rancen kuɗi kafin ya samu naira miliyan 3,980, wanda ya baiwa faston domin ya sauƙaƙa masa komawa ƙasar Canada.

“Bayan an daɗe ana jira ba tare da wani sakamako ba, mai roƙon ya fusata kuma ya fara tambayar wahayin faston, wanda hakan ya sa ya nemi a mayar masa da ƙuɗinsa.

“Ya bayyana cewa duk ƙoƙarin da kuma roƙon wanda ake zargin ya mayar da kuɗinsa bai haifar da wani sakamako mai kyau ba,” inji kakakin EFCC.

Ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?