Back

EFCC ta kama mutane 40 da ke damfarar gidan yana a Abuja

Jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) a ranar Juma’a, 31 ga Mayu, 2024, sun kama mutane 40 da ake zargi da damfarar gidan yana a sassan Abuja daban-daban.

Wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya fitar ta bayyana cewa an kama 18 daga cikin waɗanda ake zargin ne a yankin Dawaki, yayin da sauran 12 aka kama a wasu wurare na Abuja.

Ya ce kama su ya biyo bayan sahihan bayanan sirri game da zargin da ake musu na hannu a laifukan gidan yana.

A cewar Oyewale, an kama wayoyi 23, kwamfutar tafi-da-gidanka huɗu da kuma motoci huɗu daga hannun waɗanda ake zargin.

Ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?