
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce ta kwato sama da Naira biliyan 30 daga cikin N37,170, 855,753.44 da ake zargin an wawure a ma’aikatar jin kai a karkashin tsohuwar ministar, Sadiya Umar-Farouk.
Majiyoyi a EFCC, wadanda suka zanta da wakilinmu a ranar Lahadi, sun ce hukumar ta kuma gano sama da Naira miliyan 500 daga cikin ‘kudade da aka karbo’ da ke da alaka da magajiyar Umar-Farouk, Betta Edu, wadda Shugaba Bola Tinubu ya dakatar a kwanakin baya.
A watan Disamba ne jaridu suka ruwaito cewa an fitar da N37,170,855,753.44 daga asusun gwamnati tare da aika su zuwa asusun banki daban-daban har guda 38 Wadanda ba na gwamnati ba da ke cikin wasu manyan bankunan kasuwanci mallakar ko kuma Wanda ke da alaka da wani dan kwangila, James Okwete.
An tattaro cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne hukumar EFCCn ta kwato N30bn biyo bayan sanya hannun jari a asusun bankin Umar-Farouq da Okwete, wadanda har yanzu jami’an hukumar da ke binciken cin hanci da rashawa ke ci gaba da binciken su.
Har ila yau hukumar na ci gaba da garkame Edu dangane da badakalar Naira biliyan 17, yayin da ita ma Ko’odinetar shirin zuba jari ta kasa, Halima Shehu, ita ma tana ci gaba da amsa tambayoyi.
Wata majiya ta EFCC ta bayyana cewa, “Hukumar a yanzu ta kwato sama da N30bn daga cikin N37.1bn da aka wawure Wadanda aka alakanta da tsohuwar Minista Sadiya Umar-Farouq.
“Mun samu nasarar kwato kudaden ne bayan da muka sanya lamuni a asusun ajiyar tsohuwar ministar da kuma dan kwangilar, Mista Okwete, wanda ake alakanta shi da badakalar da ake bincike. Duk ministocin da dan kwangilar har yanzu masu bincikenmu na gasa su a kowace rana.”
Wani babban mai bincike a EFCC ya kara da cewa, “Mun sake gano wasu makudan kudade da suka kai N17bn daga ma’aikatar jin kai, kuma bisa zargin damfarar na ministar da aka dakatar, Betta Edu, ya zuwa yanzu mun kwato sama da N500m. Har yanzu Edu tana amsa tambayoyi game da lamarin.
Da aka tuntubi kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale domin jin ta bakinsa, yace, “Har yanzu kuma ana gasa mai kula da NSIPA, Halima Shehu.”