
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), za ta gurfanar da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, a gaban Mai Shari’a Sylvanus Oriji na Babbar Kotun Birnin Tarayya (FCT), Maitama ranar Alhamis.
Sirika, minista ne a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, za a gurfanar da shi a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume shida da aka yi wa gyara.
Za a gurfanar da shi ne tare da wasu mutane uku da suka haɗa da ‘yarsa Fatima; Jalal Hamma da Al-Duraq Investment Ltd, bisa laifin zambar da ta kai naira biliyan 2.7.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya bayar da rahoton cewa, a wani ɓangare na binciken hukumar EFCC kan almundahanar kuɗi da ake zargin tsohon ministan ya aikata, “ciki har da zambar kwangilolin da ma’aikatar ta bayar a ƙarƙashin sa, a ranar 23 ga Afrilu, hukumar ta tsare shi a Abuja’’.
Hukumar, shiyyar Abuja, ce ta gayyaci Sirika kan zargin zambar kwangila, kuma ba tare da ɓata lokaci ba aka yi masa tambayoyi aka tsare shi a ofishin shiyya ta 2 na Hukumar a titin Formella, Wuse 2.
Wata majiya ta EFCC da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa NAN cewa “Tsohon Ministan (Sirika) ya samu gayyata domin yi masa tambayoyi daga masu binciken da ke kula da zambar kwangilar da ake zargi a ƙarƙashin sa a ma’aikatar. Ya mutunta gayyatar kuma yanzu haka an tsare shi.”
Majiyar ta kuma ce hukumar EFCC ta daɗe tana binciken zambar kwangilar da ake zargi yayin da ministan yake kan muƙaminsa, har ma ya gana da masu bincike kafin a tsare shi.
NAN ta ruwaito cewa tun da farko an shirya ci gaba da shari’ar a ranar Talata amma saboda roƙon da EFCC ta yi na gyara tuhume-tuhumen, an bayar da sabuwar rana.