Back

El-Rufai bai taɓa son muƙamin minista ba, inji ɗansa

Bello El-Rufai

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazaɓar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai, ya ce Nijeriya ta rasa ƙwararren mai gudanar da mulki kamar mahaifinsa, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, bayan da Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da naɗin sa na minista.

Bello sai dashi ’yan wasa suka roki mahaifinsa domin ya amince da nadin mukamin minista daga Shugaba Bola Tinubu.

Maganar gaskiya, ba ya son aikin. Mun tabbatar masa da cewa, Asiwaju zai samar da kyakkyawar tawaga kamar yadda ya yi a Legas.

“Shugaban Ƙasa ya so yin aiki da shi. Ya tabbatar da hakan lokacin da ya zo Kaduna. Mun san aikin da za’a bashi na iskar gas ne da wutar lantarki. Ya nanata wa Shugaban Ƙasa a cikin sirri cewa Nijeriya ba za ta warware matsalar wutar lantarki ba idan ba a sa iskar gas a ƙarƙashin sauran ɓangarorin wutar lantarki ba.

“Abin ban mamaki shi ne babu wani abu da ya fi rashin wutar lantarki a makonni biyu da suka gabata. Na ji takaici saboda Nijeriya ta yi rashin ingantaccen shugaba kamar mahaifina, wanda ke shirye ya tsai da shawarwari masu wahala don magance wata matsala.”

Bello, ya ci gaba da cewa ‘yan Nijeriya da dama ba su san mahaifinsa da gaske ba. Ya ce, “Mahaifina mutum ne mai sauƙaƙan ra’ayi wanda mutane ke da ra’ayi da yawa akan sa. Na samu faifan bidiyonsa inda mutane ke faɗin wannan ko wancan a kansa ba tare da saninsa ba.

“Mahaifina ba ya ƙoƙarin canza ra’ayin mutane game da shi. Bai wani damu ba.

“Akwai tunanin cewa shi mai adawa da Kirista ne. Amma, wanda ya fi kusanci da shi tun da mu (‘ya’yansa) ke da shekara huɗu, wani mutum ne ɗan Jihar Kuros Riba, Peter Jones.

“A matsayinsa na Ministan Babban Birnin Tarayya, ya rusa masallatai. Limamin ya ce ya tsani Musulunci. Ya rusa majami’u kuma Kiristocin sun ce ya tsani Kiristoci. Wataƙila, limamai da fastocin ne ke da matsala ba shi ba.”

Ya ƙara da cewa mahaifin nasa yana da kura-kurai da yawa ta fuskoki da dama, inda ya ce, duk da haka, yana cikin haziƙan masu gudanarwa kamar Dora Akunyili, Ngozi Okonjo Iweala, Nuhu Ribadu, Charles Soludo da Akinwunmi Adesina.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?