
Aliko Dangote
Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, ya koka kan yadda faɗuwar darajar naira ya kasance babbar matsala ga kamfaninsa a shekarar 2023.
Dangote, Shugaban Kamfanin Dangote, ya bayyana haka ne a lokacin babban taron shekara-shekara na Matatar Sukari na Dangote Plc.
A cewar hamshaƙin attajirin, yanayin gudanar da harkokin kasuwancinsa a cikin gida ya kasance matsananci, kasancewar shekarar ta zaɓe ce da aka rantsar da sabuwar gwamnati.
Dangote ya ba da tabbacin cewa, kamfanin na yunƙurin biyan masu hannun jari riba na wannan shekarar.
Ya bayyana cewa, kamfanoni da dama a Nijeriya, musamman ma harkokin kasuwancin abinci da abin sha, suma abin ya shafe su kuma sun kasa biya.
“Muna yin duk abin da ya dace don ganin cewa za mu dinga biyan masu hannun jari riba domin idan aka duba ribar da muka samu a bara ya kai kusan fiye da kashi 50 cikin 100, don haka za mu yi ƙoƙari mu fita daga cikin matsalar.” inji Dangote.
“Babban matsalar da aka samu a zahiri shine faɗuwar darajar naira daga naira 460 zuwa naira 1,400. Kusan kashi 97 cikin 100 na kamfanoni, musamman a harkar abinci da abin sha, babu wani daga cikinsu da zai biya riba a bana amma, za mu yi ƙoƙari mu fita daga cikinsa da wuri.
“Muna so mu ga cewa komai ƙanƙantarsa, za mu iya biyan riba, musamman ma idan naira ya farfaɗo.
A bara, Dangote ya sanar da asarar naira biliyan 164 na canjin kuɗaɗen waje saboda taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar musamman daga faɗuwar darajar naira.