Back

Fadar shugaban kasa ta musanta ƙin amincewar ƙasar Qatar da ziyarar Tinubu 

Qatar ta ki amincewa da ziyarar da shugaban kasa Bola Tinubu zai yi kan harkokin kasuwanci da zuba jari.

Ofishin jakadancin kasar Qatar da ke Abuja ya bayyana hakan a wata wasika mai dauke da kwanan wata ashirn da biyu ga wannan watan wadda kuma ofishin ya aikewa sashen kula na ma’aikatar harkokin Ƙasashen wajen Najeriya.

An shirya ziyarar shugaban kasa Tinubu zuwa ƙasar ta Qatar ne tun baya, a ranakun biyu da kuma uku ga watan uku na wannan shekarar.

Amma a cikin wasikar, wacce ma’aikatar Ƙasashen wajen Najeriyan ta samu daga ofishin jakadan ƙasar ta Qatar, a ranar ashirin da biyu ga wannan watan, Ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu ta Qatar ta nemi afuwar kin amincewa da ziyarar.

Wasiƙar ta ci gaba da cewa, “game da ziyarar da mai girma Bola Ahmed Tinubu, Shugaban kasar Najeriya zai kawo Qatar daga biyu zuwa uku ga wata mai zuwa wadda ke kunshe a wasiƙa Mai lamba: Ref: ME.631 2024 da kwanan wata she biyu ga watan biyu na wannan shekarar, wadda aka shirya ziyarar kasuwanci da zuba jari ….

“Mai girma ministan kasuwanci da masana’antu na ƙasar Qatar zai gudanar da wasu aiyuka a wajen kasar a dai-dai lokacin da Najeriya ta shirya ziyarar.

Wasiƙar na kunshe da cewa, “Ofishin Jakadancin yana mai farin cikin sanar da cewa ma’aikatar kasuwanci da masana’antu ta Qatar na neman afuwa, ba za ta iya gudanar da taron kasuwanci da zuba jari ba kamar yadda bangaren Najeriya ya tsara.”

Ofishin jakadancin ya na cewa “babu wata yarjejeniya da kasar Qatar da Tarayyar Najeriya suka rattaba hannu kan inganta zuba jari da kuma kariya.”

Ta ce, “Jahar Qatar za ta karbi bakuncin wani taron koli da za a yi ta yanar gizo a lokacin da aka ware cewa Tinubu zai Kai ziyarar, kuma hankalin hukumomin jihar zai tattara ne kan wannan taron.”

Sai dai fadar shugaban kasar Najeriyan ta ce gwamnatin Qatar ba ta yi watsi da ziyarar Tinubu ba.

A cikin wata sanarwa da babban mai baiwa shugaba Tinubu shawara na musamman kan hakkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar ransar Asabar ya bayyana cewa, taron zuba jarin da ya kunno kai tsakanin ‘yan kasuwan Najeriya da na Qatar daya ne kawai daga cikin al’amura da dama da aka shirya gabannin ziyarar shugaba Tinubu a kasar ta larabawa.

Ya ce, Ziyarar da shugaba Bola Tinubu zai kai kasar Qatar ya biyo bayan gayyatar da Sarkin Qatar, mai martaba Sheik Tamim Bin Hamad Al-Thani ya yi wa shugaban Najeriyan ne.

Ya Kara da cewa ba daidai ba ne wani ya kirkiro labarin kanzon kurege yai nuni da cewa hukumomin Qatar sun yi watsi da zuwan shugaban Najeriya ƙasar game da wani taron kasuwanci da zuba jari wanda ke da nasaba da ziyarar shi kasar mai muhimmanci.”

Onanuga, a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Ziyarar da shugaban kasa Bola Tinubu ya kai Qatar,. A matsayin martani da ya yi, yana cewa ma’aikatun harkokin wajen kasashen biyu sun bayyana cewa, ana sa ran Tinubu zai tafi Qatar ziyarar aiki kamar yadda aka tsara, Kuma Shugaban na Najeriya zai tattauna da shugaban kasar Qatar kan muhimman batutuwan da suka shafi diflomasiya da tattalin arziki.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?