Back

Falana ya yi barazanar maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan ƙarin kuɗin wutar lantarki

Launyan Kare Haƙƙin Bil’adama, Femi Falana

Lauyan Kare Haƙƙin Bil’adama, Femi Falana (SAN), ya yi barazanar maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi wa kwastomomin da ke samun wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 20 wato Band A a Nijeriya.

Falana wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake magana kan al’amuran da suka shafi harkar wutar lantarki a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels ya ce Gwamnatin Tarayya da kuma Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, sun ƙara kuɗin wutar lantarki ba bisa doka ba.

Falana ya bayyana cewa babu tallafin wutar lantarki kuma ya yi zargin cewa gwamnati na ƙoƙarin tara wa Kamfanonin Raba Wutar Lantarki (Discos) da ba su da kuɗi kuɗaɗe.

Babban Lauyan na Nijeriya ya yi zargin cewa tuni Gwamnatin Tarayya ta cire tallafin wutar lantarki a shekarar 2022 don haka gwamnati ta sabon ƙarin kuɗin wutar lantarki ta sa ‘yan Nijeriya su biya kuɗin rashin inganci da rashin iya aiki na masu tafiyar da harkar wutar lantarki.

“Tallafin wutar lantarki ya ƙare ne a shekarar 2022. Gwamnati na sa ‘yan Nijeriya su biya kuɗin rashin inganci da rashin iya aikin masu kula da harkar wutar lantarki.

“Na yi nazari kan tanade-tanaden Dokar Samar da Wutar Lantarki ta shekarar 2023 kuma ba zan iya tantance rawar da Ministan Wutar Lantarkin zai taka ba dangane da ƙarin kuɗin wutar lantarki.

“Wannan shi ne keɓaɓɓen alhakin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya. Kuma bisa ga doka, ba za a iya tabbatar da ƙaruwar ba a ƙarƙashin Dokar Samar da Wutar Lantarki, musamman, sashi na 116 na dokar ya tanadi cewa mai lasisin da ya yi aiki yadda ya kamata za a ba shi damar dawo da wani ɓangare, ko cikakken kuɗin ayyukansa na kasuwanci.

“Babu wanda zai ce a yau cewa DisCos na gudanar da aiki yadda ya kamata a Nijeriya har haka. Ba a cika tanadin dokar ba.

“Na biyu, domin a ƙara kuɗin wutar lantarki a ƙasar nan, shawarar mai lasisi (DisCos) za a buga shi a cikin jaridar Gwamnatin Tarayya da kuma manyan jaridu a cikin ƙasar nan da nufin faɗakar da masu amfani da wutar lantarki da sauran masu ruwa da tsaki a lamarin ko za su ƙalubalance lamarin,” inji SAN.

Yayin da ya ke cewa masu ruwa da tsaki na da kwanaki 30 don gabatar da ƙorafi, kamar yadda doka ta ce, Falana ya ce dole ne a yi la’akari da waɗannan ƙorafe-ƙorafe a wani taron jin ra’ayin jama’a da hukumar za ta yi.

“Lokacin da aka yi yarjejeniya sosai za a ba da izinin ƙara kuɗin wutar lantarki,” inji shi.

Falana ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta sake tunani kan sabuwar tsarin wutar lantarki ta koma yadda ake a da, ya ƙara da cewa hakan zai ƙara talauta talakawa.

“A lokacin da ya dace, idan ba a mayar da martani ba, sai mun garzaya kotu domin gwamnati ta yi gargaɗi, ministan ya yi gargadi cewa ƙarin kuɗin da aka yi a wannan karon zai samar ma gwamnati ko discos naira tiriliyan 1.6 ne kawai, yayin da naira tiriliyan uku ne.

“Don haka, talakawan da ministan ke magana a kai, sauran tawaga, nan ba da jimawa ba, gwamnati za ta ƙara musu ƙarin kuɗin domin a dawo da naira tiriliyan 1.4 da ministan ke magana a kai,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?