Back

Faransa ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta ba mata ‘yancin zubar da ciki

Majalisar Faransa a ranar Litinin

Faransa ta kafa tarihi, inda ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta ba mata ‘yancin zubar da ciki a kundin tsarin mulkin ta.

A ranar Litinin ‘yan Majalisar Dokokin Faransa suka amince da dokar da gagarumin rinjaye, da ƙuri’u 780-72.

Wannan ƙuri’ar ta tabbatar da dokar wadda ta bayyana “tabbataccen ‘yanci” don zubar da ciki a Faransa.

Wannan abu ya faru ne a daidai lokacin da batun zubar da ciki ke fuskantar ƙalubale a duniya, ciki har da Amurka da wasu sassan Turai.

Faransa ta fara halasta zubar da ciki a shekara ta 1975. Yanzu da yake cikin kundin tsarin mulkin ƙasar, haƙƙi ne da aka amince da shi wanda wata gwamnati ko wata sabuwar doka ba za ta taɓa soke shi ba.

An haskaka Hasumiyar Eiffel da ke Paris da gagarumin taken “jikina, zaɓina” bayan da aka kaɗa ƙuri’ar.

Firayim Minista Gabriel Attal ya jaddada muhimmancin matakin, ya bayyana cewa ya kamata ne ‘yan Majalisar Dokokin su mutunta gwagwarmayar mata da a baya suka fuskanci zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba wanda ke da haɗari.

Ya ƙara jaddada cewa, “Fiye da komai, muna isar da saƙo ga dukkan mata: Jikin ku naku ne.

Shugaba Macron kuma ya bayyana cewa za a gudanar da wani biki a Ranar Mata ta Duniya (ranar 8 ga Maris) don tunawa da gyaran dokar.

Sai dai kuma Cocin Katolika ya ci gaba da yin adawa da matakin. Cibiyar Kare Rayuwar Bil’adama (Pontifical Academy for Life), ta bayyana matsayar ta cewa “a lokacin da ake kare haƙƙin bil’adama, babu ‘yancin ɗaukar rayukan bil’adama.”

Wannan ra’ayi ya fito ne daga taron limaman Kiristanci na Faransa kafin a kaɗa kuri’a.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?