Aƙalla shaguna sha takwas ne aka tabbatar sun lalace sakamakon fashewar iskar gas da ta afku a hanyar Agbado da ke unguwar Toyin a ƙaramar hukumar Ifako Ijaiye a jihar Legas da yammacin ranar Talata.
Daraktar Hukumar Kashe Gobara ta jihar Legas, Margaret Adeseye, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta bawa manema labarai ranar.
wasu shaguna da kayayyaki da har yanzu ba a tantance adadin su ba sun lalace a gobarar da ta afku a lokacin da wata tankar gas ta kama da wuta a yankin.
Da yake bayar da ƙarin bayani kan gobarar, Adeseye ya ce fashewar ta afku ne sakamakon silindan gas guda shida masu nauyin kilo Saba’in da biyar zuwa hamsin da ake saukarwa daga wata ƙaramar mota a gidan mai.
Ta ƙara da cewa gobarar ta bazu zuwa gefen titi, inda ta lalata jimillar shaguna sha takwas da kayan da ke cikin su tare da ƙaramar motar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Musabbabin lamarin na da nasaba ne da sauke manyan silindan gas guda shida masu girman 75-50 (kg) daga wata ƙaramar mota da aka ajiye zuwa wani shagon gas wanda bisa kuskure ya yi sanadin fashewa daga hular silinda guda ɗaya da ya lalace wanda wuta ya taɓa.
“Gobarar da ta biyo baya ta tashi zuwa ɗaya gefen titin da taimakon ɗaya daga cikin silidan gas ɗin da ya bi ta kan titin, wanda ya shafi shaguna sha takwas gaba ɗaya da abinda ke ciki tare da ƙaramar motar.”
Adeseye ya ce babu alamun asaran rayuka ko rauni.