
Wasu fusatattun matasa sun tarwatsa zanga-zangar da masu sana’ar kifi suka yi, tare da sace kayan abinci a manyan motoci da suka makale a kan titin Kaduna a yankin Suleja a jihar Neja.
Da yake tabbatar da hakan ga ga ‘yan jaridars a yau ranar Alhamis, dan takarar majalisar tarayya a jam’iyyar PRP na mazabar Suleja, Sadiq Bala, ya ce masu sana’ar kifin suna nuna rashin amincewar su da karin farashin kifi ne a lokacin da abin ya faru.
Bala ya ce masu sayar da kifin sun fara zanga-zangar ne da misalin karfe goma na safiyar yau Alhamis.
“Masu sayar da kifi ne suka fara zanga-zangar sai fusatattun matasa suka mayar da ita zanga-zangar wahala,” in ji shi.
“A cewar rahoton da na samu daga wurin, farashin katan kifi ya kai Naira dubu talatin da hudu a jiya amma da safe farashin ya tashi zuwa naira dubu srna’,in da takwas, sanadiyyar zanga-zangar kenan biyo bayan karin kudin.”
“Wasu masu wucewa ne suka zo suka mamaye zanga-zangar. Sun tare hanyar Abuja zuwa Kaduna, wanda hanya ce mai cike da cunkoso.”
“Eh, sun fara da abarba, sun yi garkuwa da wata jar Volkswagen dauke da abarba, amma direban ya samu tserewa.
“Akwai wasu motocin Dangote da BUA a kan hanya. Sun daka wa manyan motocin wawa, suka fara satar kayan abincin da ke ciki.”
“Daya daga cikin motocin na dauke da buhunan shinkafa. Da kyar karfin suka kwacewa direban, har wasu suka fara bikin con ganima.”
“Jami’an tsaro na can. Sojoji ne suka zo, Suleja da ‘yan sandan Tafa suka je can suka fara harba barkonon tsohuwa, don haka suka samu nasarar tarwatsa masu zanga-zangar.”
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, “An yi zanga-zanga da safiyar yau a kan hanyar Kaduna zuwa Suleja, kuma ba a sanar da shirin zanga-zangar ga ‘yan sanda ba. Daga baya an gano cewa wasu bata gari ne suka tare babbar hanyar suka yi awon gaba da ksyan abincin” inji shi.
“Kwamandan yankin Suleja, ACP Sani Musa, ya hada ’yan sintiri zuwa wurin, inda suka tarwatsa masu zanga-zangar, aka kuma share babbar hanyar domin zirga-zirgar ababen hawa ya ci gaba. Duk da haka, ana ci gaba da sa ido.”
A kwanakin baya ne mazauna garin Minna babban birnin jihar Neja da kuma yankin Suleja na jihar suka yi zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a kasar.
An kuma gudanar da zanga-zanga a wasu sassan kasar nan yayin da farashin kayan abinci ke ci gaba da tashin gwauron zabi tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023.