
Hukumar Babban Birnin Tarayyar Najeriya, ta bayar da sanarwa ga ɗaruruwan waɗanda ke fakewa a ƙarƙashin gadoji a yankunan Garki, Wuse II, Maitama da Wuse a Abuja, da su gaggauta barin wuraren nan da mako guda ko kuma su fuskanci fushin gwamnati.
A cewar hukumar ta Abujan, ya kamata a ce wasu wuraren da abin ya shafa su zama wuraren da suka dace da muhalli ne amma sai suka rikiɗe zuwa unguwannin marasa galihu da jama’a ke zama tare da aiwatar da munanan ayyuka a cikin birnin.
Dokta Fred Kpakol, Babban Mataimaki na Musamman (SSA) kan Kula da Muhalli ga Ministan Babban Birnin Tarayyar, wanda ya bayyana hakan, ya koka da cewa ƙarƙashin gadajen da abin ya shafa basu da kyan gani.
Ya ce mutane na ƙona itace a wuraren wanda hakan kamar yadda ya ce zai shafi rayuwar su kuma daga ƙarshe ya kawo rugujewar gadojin.
Kpakol ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya jagoranci jami’an Hukumar Kare Muhalli ta Abuja (AEPB) domin wayar da kan mazaunan a kan matsalar lafiya da taɓarɓarewar tsaro, inda ya bayyana cewa mazauna wannan wuraren zasu iya kamuwa da cututtuka har I zuwa rasa rayuka.
Ya kuma gargaɗi waɗanda ke zaune a ƙarƙashin gadojin a sassa dabam-dabam na birnin da su fice saboda za su gudanar da aikin kawar da duk wani ɓata gari da mutanen da bai kamata su kasance a wuraren ba a ƙarshen wa’adin.
Ya ce: “Za a yi amfani da cikakken ikon doka. Shi ya sa muka ba su mako guda su fita daga waɗannan wuraren, domin za mu riƙa tafiya daga wuri zuwa wuri, kuma za mu tabbatar an sanya abubuwa a inda suka dace.
“Kuna sane da yawaitar sace-sacen mutane da sauran munanan ayyuka da mutane ke yi daga wurare daban-daban sannan su gudu ƙarƙashin gadoji, suna fakewa ƙarƙashin guraren marasa galihu da ke can, wanda hakan ba za a amince da shi ba.
“Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana shirin baiwa jama’a wani Sabon Fata, ta hanyar kayan aiki dake hannun Ministan Babban Birnin Tarayya, Barista Nyesom Wike, wanda ya shirya don tsaftar garin, kuma domin wannan birni ya kasance mai tsafta, dole ne a magance guraren marasa galihu irin wannan.
“Saboda tsaron wannan birni yana da matuƙar muhimmanci a matsayin sa na fuskar Najeriya, kuma ba za mu iya ɓata ƙasar nan ba, muna so mu yi gargaɗin cewa duk wani mutum da ya zo nan ya zauna dole ne ya bar wurin…”
Dangane da matakin wayar da kan mazaunan kafin a kore su, mai taimaka wa Ministan ya ce: “Wannan gwamnati tana da fuskar mutane, shi ya sa muke so mu roƙe su, ta hanyar yin magana da lamirinsu cewa babu buƙatar su yanke fata ko jin cewa idan ba su da abin yi, to sai su zauna a ƙarƙashin gadoji. Wannan aiki ne na kashe kai, domin za a iya samun ɓarkewar annoba da za ta iya cinye su duka.
Dangane da roƙon da gwamnati ta yi ta samar musu da wani wuri na dabam, Kpakol ya ce akwai hukumomin da za su iya tuntuɓar su domin yi musu ɗauki amma ya tunatar da su cewa gwamnati ba za ta iya yin komai ba.
Mataimakin Daraktan Sa Ido da Tabbatar da Doka na AEPB, Kaka Bello, ya yi gargaɗin cewa za a aiwatar da aikin tare da hukumomin da abin ya shafa a wasu gadojin da ke kan titin Ahmadu Bello Way, Ademola Adetokumbo Way, Wuse II da Parkway, da ke yankin Kasuwar Wuse a lokacin karewar wa’adin.
Bello ya bayyana cewa wasu daga cikin fitattun wuraren sun haɗa da gadar da ke kusa da Transcorp Hilton a kan hanyar Ademola Adetokumbo, titin shaƙatawa na kusa da Kasuwar Wuse, gabanin gadar Kashim Ibrahim, gadar kan titin Ahmadu Bello da ke kusa da Junction Bankin Diamond da gabanin gadar Area 11, inda akwai masu sana’ar hannu da yawa.
“Ko da yake mun sami nasarar kawar da su, ana iya ganin cutarwar da aka yi wa waɗannan ababen more rayuwa a fili. Za mu aiwatar da aikin da ake buƙata don haka muna kira gare su da su bar dukkan gadojin…,” in ji shi.
Wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun danganta ci gaba da mamaye gadojin da taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar.
Sun yi kira da babbar murya ga gwamnati da ta taimaka musu don samun wani wurin da za su koma, domin ci gaba da sana’o’insu.
Ga wata Iya Gizo da ta bayyana kanta a matsayin mai takaba daga jihar Nasarawa, ta san illar zama a ƙarƙashin gadar amma ba ta da wani zaɓi.
Har ila yau, wani mai sana’ar hannu da ke aiki a ƙarƙashin gadar, kusa da City Park a Wuse II, Emmanuel Abraham, ya koka da cewa, aikin share fage ba wai kawai zai kawar da shi da sauran masu fafutukar rayuwa ba ne, illa ƙara jefa su cikin mawuyacin hali na barazanar tsaro da tattalin arziƙi da ke addabar birnin.