
Gawarwakin Wigwe, matarsa, da ɗansa
Gawar marigayi shugaban rukunin kamfanonin Access Holdings kuma tsohon manajan daraktan Bankin Access, Herbert Wigwe, da na matarsa da ɗansa sun iso Nijeriya.
Gawarwakin nasu sun isa filin jirgin sama na Port Harcourt daga ƙasar Amurka a ranar Juma’a.
Za a yi jana’izar su a ranar Asabar a mahaifarsa, Isiokpo, a ƙaramar hukumar Ikwerre ta jihar Ribas.
Wigwe, tare da matarsa, ɗansa, da Abimbola Ogunbanjo, tsohon Manajan Darakta na Hukumar Musayar Kuɗaɗe ta Nijeriya (NGX Group), sun mutu a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a kan iyakar Nevada da California a Amurka a watan jiya.
Tun bayan mutuwarsu, ana ci gaba da karrama Wigwe yayin da masu tausayawa suka tuna da ayyukansa yayin da yake raye.