Back

Gawarwakin jami’an soji 17 da aka kashe a Delta sun isa maƙabartar sojoji a Abuja

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta a ranar 14 ga Maris, 2024, sun isa Maƙabartar Sojoji ta Ƙasa, Abuja, inji rahotonni.

Gawarwakin waɗanda suka isa da misalin ƙarfe 2:26 na ranar Laraba, motocin agajin gaggawa na sojoji ne suka kai su tare da rakiyar Jami’an Bayar da Agajin Gaggawa na Babban Birnin Tarayya.

An ruwaito cewa a halin yanzu manyan jami’an soji daga sassa daban-daban a faɗin ƙasar nan sun halarci wajen domin karrama jaruman da suka mutu.

‘Yan uwa da abokan hulɗar ​​ma’aikatan da suka mutu da kuma matan wasu jami’an soji su ma suna nan a wajen. Kuma ana sa ran Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu zai halarci jana’izar.

An ruwaito yadda wasu fusatattun matasa suka kai wa sojojin Bataliyar Amphibious 181, ƙaramar hukumar Bomadi jihar Delta farmaki suka kashe su yayin da suke aikin zaman lafiya a yankin Okuoma.

Lamarin ya faru ne lokacin da sojojin suka amsa kiran gaggawa bayan rikicin ƙabilanci tsakanin al’ummar Okuoma da Okoloba duk a Delta.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?