Back

Gawawwaki sun ruɓe a ɗakunan ajiye su na Sojoji yayin da kamfanin wutar lantarki ya katse wutar kan bashin fiye da biliyan arba’in

Gawawwakin da ke ɗakin ajiye gawawwaki na wasu barikokin sojojin Najeriya na ruɓewa saboda katsewar wutar lantarki.

Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, domin neman shiga tsakani.

Ku tuna cewa Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) ya baiwa Ma’aikata, Sassa da Hukumomin gwamnati guda tamanin da uku a yankinsa wa’adin kwanaki goma don biyan bashin Naira biliyan arba’in da bakwai da miliyan ɗari da kamfanin ke bin su ko kuma a yanke wuta.

Fadar shugaban kasa dai na cikin waɗanda ake bi bashi, amma shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kutsa kai nan take bayan an bayar da wa’adin.

Shugaban ya bada umarnin a biya basussukan.

A ziyarar da ya kai wa Ministan, Lagbaja ya yi nadama kan yadda wasu bariki da sansanin soji suke cikin duhu tun watan Janairu.

“Ana saka bashin da ake bi a kan mita, don haka duk adadin kuɗin da muka sanya, mitocin suna karɓewa nan take… Gawarwakin da ke cikin ɗakin ajiyar gawarwakin sojoji na ruɓewa kuma masu gawarwakin suna zanga-zanga,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa ba zai yiwu Sojoji su samu kuɗaɗen da za su biya gaba ɗaya basussukan da ake bin su ba tare da neman su sayar da kadarorin su domin su biya bashin kamar yadda shugaban ƙasa na wancan lokacin ya yi a shekarar 2005.

Ya kuma ba wa ministan tabbacin goyon bayan sojin ƙasar wajen samar da dabarun leƙen asiri don daƙile matsalar ɓarnar ababen wutar lantarki.

Adelabu ya tabbatar wa rundunar sojin Najeriya a shirye ya ke ya tattaunawa da Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki (DisCos) domin samun mafita daga matsalar.

A cewar Mataimaki na Musamman kan Harkokin Sadarwa da Hulɗa da Manema Labarai na Ministan, Bolaji Tunji, Adelabu ya nanata muhimmancin sayar da kadarori da samar da kudade a fannin, inda ya ƙara da cewa idan har ba a iya rage basussukan ba, zai sa baki domin a sake fasalin biyan basussukan idan har akwai tabbaci sojojin zasu dinga biyan bashin akai-akai.

Ya kuma bayyana cewa basussukan da kamfanonin rarrabawa da na Samar da Wutar Lantarki (GENCOs) ke bi ba shine kawai ƙalubalen da ke kawo cikas ga harkar wutar lantarki ba, ya ƙara da cewa ɓarnatar da kayayyakin wutar da ke haifar da rugujewar hanyoyin sadarwa na ƙasa, sata, rashin lissafi da karɓan kuɗin wuta yadda ya dace, rashin tazarar mitoci, ƙarancin iskar gas, fasa tashoshin watsa lantarki da bama-bamai a wuraren da ba su da zaman lafiya duk wani ɓangare ne na matsalolin da ake fuskanta a ɓangaren wutar lantarki.

“Matsalolin wutar lantarki sun faro ne tun shekaru hamsin da suka gabata kuma gwamnatin da ba ta wuce watanni takwas ba ba za ta iya amfani da sihiri don samar da mafita ba. Akwai wata karin magana cewa ba za ku san abin da ke faruwa a Roma ba har sai kun isa Roma, ”in ji shi.

Ministan wanda ya yarda cewa ba kawai barikokin sojoji aka katsewa wutar lantarki ba amma matsalar ƙasa ce gaba ɗaya ya ce DISCOs da GENCOs kamfanoni ne masu neman riba.”

Muna iya roƙonsu ne kawai da su ɗauki tsarin biyan kuɗi a kowane wata maimakon sanya dukkan basussukan a cikin mitar su,” in ji shi.

Yayin da yake ƙarfafa rundunar Sojoji da su ci gaba da taimakawa ma’aikatar wajen kula da ababen samar da wutar lantarki a faɗin kasar nan, Ministan ya yi alƙawarin neman haɗin gwiwa ga rundunar ta hanyar duk wani abokan hulɗar ci gaba don dasa na’urar sola don samar da wutar lantarki a bariki da sansanin sojoji.

Tun da farko dai babban hafsan sojin ya bayyana cewa, babban dalilin da ya sa suka kai ziyarar shi ne domin tattauna illar rashin wutar lantarkin da ake samu a sassan sojoji da kuma hanyar da za a bi domin a samu mafita.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?